Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

  • Gwamnan jihar Oyo ya shawarci 'yan Najeriya kan wasu tsirarun 'yan siyasan da ke nuna sha'awar gaje kujerar Buhari
  • Ya ce, bai kamata 'yan Najeriya su tsaya su zabi wanda ba zai tsinana musu komai ba, su zabi mai jini a jika shi ne daidai
  • Ya kuma ce, ya kamata su tsofaffin 'yan siyasar su zauna su yi tunani kafin bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar 2023

Jihar Oyo - Jaridar The Cable ta rahoto cewa, Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya ce ‘yan takarar da ke da “jini a jika” na mulkar Najeriya ne kadai ya kamata a zabe su a zaben 2023 mai zuwa.

Da yake magana a ranar Talata a wurin bikin ritayar da aka yi na karrama Samson Ayokunle, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Makinde ya ce mulki ba abu ne mai sauki ba.

Kara karanta wannan

Buhari: Ka da 'Yan Najeriya su cire tsammani daga Super Eagles

Gwamna Makinde ya caccaki tsoffi masu neman mulki
Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsoffin 'yan siyasan da ke hango kujerar Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Ya shawarci masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekarunsu na 70 da su yi tunani mai zurfi game da shawarar da suka yanke.

Ya bukaci al’ummar Oyo da ‘yan Najeriya baki daya da su zabi wadanda suke da karfin yi wa kasa hidima da gaske.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Tribune ta rahoto Makinde yana cewa:

"Mun ga dattijai da yawa da ke son mulkin kasar da ke da shekaru 75 ko 78. Ina so su yi tunani mai zurfi ina gaya wa mutanen jihar Oyo da Najeriya cewa duniyar nan ba ta da sauki."
“Yana yiwuwa ku ba da wakilci, ku nemi mutane su zagaya ko’ina amma idan sun kawo muku rahoto, idan ba a kara wani abu ba, watakila an cire wasu abubuwa.
"Muna cikin lokacin zabe a zahiri kuma abin da zan ce mana a matsayinmu na jama'a shi ne cewa muna bukatar mu yi zabi cikin hikima da zaben mutanen da ke da karfin da za su yi wa kasa hidima."

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Bola Tinubu, jigo a jam’iyyar APC, mai shekaru 69, na daya daga cikin mutanen da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Makinde ya shaida wa Tinubu lokacin da ya ziyarce shi jihar Oyo a ranar 15 ga watan Janairu cewa Najeriya na bukatar “mafi kyawu ne kawai a wannan lokacin” don tafiyar da ita.

A halin da ake ciki, wasu da suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa sun hada da Dele Momodu, dan jarida kuma mawallafin Mujallar Ovation; da Chukwuka Monye, ​​kwararre kan harkokin canji.

Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023

Kungiyar Miyatti Allah ta Najeriya (MACBAN), ta ce bata goyon bayan kudirin takarar shugabancin kowani dan takara a babban zaben 2023.

Babban sakataren MACBAN, Alhaji Baba Ngelzarma, ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, a Abuja, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Ngelzarma ya ce kungiyar tana mutunta takarar dukkanin yan takarar shugaban kasa sannan cewa lokaci bai yi da za ta fitar da wanda zata marawa baya ba, rahoton Daily Post.

Asali: Legit.ng

Online view pixel