Nasara daga Allah: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun gwarazan yan sanda a Katsina

Nasara daga Allah: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun gwarazan yan sanda a Katsina

  • Wasu yan bindiga da suka yi yunkurin aikata ta'addanci a Katsina, sun kwashi kashin su a hannun gwarazan yan sanda
  • Jaruman hukumar yan sanda reshen jihar sun samu nasarar dakile harin yan ta'addan kuma sun kwato dabbobin da suka sace
  • Yanzun haka sun bazama cikin daji domin kamo yan ta'addan ko kuma gano gawarwakinsu bayaɓ musayar wuta

Katsina - Gwarazan yan sanda sun dakile harin yan bindiga, waɗan da suka farmaki ƙauyen Faɗimawa a karamar hukumar Kurfi, jihar Katsina.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kastina, Gambo Isa, ya tabbatar da haka ranar Jumu'a, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa yan ta'addan sun shiga da sanyin safiyar ranar Alhamis, kuma suka sace adadi mai yawa na dabbobin jama'a.

Jihar Katsina
Nasara daga Allah: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun gwarazan yan sanda a Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da aka sanar da yan sandan Kurfi, nan take suka kai ɗauki ƙauyen, suka yi musayar wuta da maharan, a wannan lokaci ne suka kwato baki ɗaya dabbobin da suka sace.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandazon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja

Yan ta'addan da ba'a san adadin su ba, sun ranta a na kare domin tsira da rayuwarsu, amma rahoto yace yan sanda sun jikkata su da harbin bindiga.

Yadda lamarin ya faru

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar ya ce:

"A ranar 27 ga watan Janairu, wasu yan ta'adda suka farmaki kauyen Faɗimawa dake ƙaramar hukumar Kurfi, inda suka sace dabbobi masu yawan gaske."
"Shugaban ofishin yan sanda na Kurfi ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa ƙauyen, kuma suka tari yan ta'addan akai batakashi."
"Dabaru da jajircewar yan sandan ta sa suka fi ƙarfin yan ta'addan kuma suka kwato dabbobin da suka sace. Mafi yawan yan ta'addan sun gudu da raunin bindiga."

Ya ƙara da cewa tuni jami'ai suka bazama cikin dazukan dake kusa da nufin kamo yan bindigan ko gano gawarwakin su.

Kara karanta wannan

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

A wani labarin kuma Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe

Yan fashi da makami sun farmaki motar dake ɗakko kuɗi ta Banki, sun kwamushe makudan kuɗaɗe a jihar Delta.

Rahoto ya nuna cewa yan fashin sun fasa motar da harsasan bindiga, yayin da suka ɗibi kudi suka yi gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel