Bayan dage ziyarar Zamfara, Buhari ya shirya zuwa jihar Nasarawa wata mai kamawa

Bayan dage ziyarar Zamfara, Buhari ya shirya zuwa jihar Nasarawa wata mai kamawa

  • Gwamnatin jihar Nasarawa ta shirya tsaf domin karbar bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Fabrairu
  • Shugaban zai kai wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu ne jihar a kwanakin 17 da 18 na wata mai kamawa
  • Gwamnan jihar ya ce tuni jihar ta shirya tsaf, ya kuma yabawa kwamishinoninsa bisa goyon bayan ayyuka a jihar

Jihar Nasarawa - Gwamnatin jihar Nasarawa ta fara shirye-shiryen karbar bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda zai ziyarci jihar a ziyarar aiki ta kwanaki biyu a wata mai zuwa.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya bayyana hakan ne jiya a yayin taron majalisar zartarwa na jihar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shugaba Buhari zai kai ziyara Nasarawa
Bayan dage ziyarar Zamfara, Buhari ya shirya zuwa jihar Nasarawa wata mai kamawa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar gwamnan, bayanai sun iso gwamnatin jihar da ke nuni da cewa shugaba Buhari zai kawo ziyara jihar Nasarawa a ranakun 17 da 18 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Don haka, Gwamna Sule ya ce an shirya isassun abubuwan da ake bukata domin tarbar shugaban kasar.

A cewarsa:

"Tare da wannan sanarwar, akwai wasu abubuwa da ya kamata mu sanya, don yiwa shugaban kasa tarba da ta dace."

Ya yabawa ‘yan majalisar zartaswa na jihar, musamman kwamishinonin da suke yin iyakacin kokarinsu wajen ganin sun taimaka wa gwamnati wajen ganin an samar da romon dimokradiyya ga al’umma.

Gwamnan ya bayyana jin dadinsa da yadda wasu daga cikin kwamishinoninsa ke taka rawa bayan rantsar da su.

Daga Sokoto, Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau

TVCNews ta ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fasa zuwa jihar Zamfara sakamakon bacin yanayi a sararin samaniya.

Shugaban kasan dai yanzu yana jihar Sokoto kuma zai koma birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari ya lula Zamfara domin jajantawa wadanda 'yan ta'adda suka yi wa barna

Buhari ya shirya kai ziyara wajen gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, don jajanta masa bisa rashin rayukan da akayi sakamakon hare-haren yan bindiga.

Hakazalika Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa Shugaban kasan ya shirya tashi daga Sokoto amma ya fasa saboda lalacewar yanayi, ruwayar DailyTrust.

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya dira a babbar tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Sokoto don kaddamar da kamfanoni.

Buhari wanda ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnati ya dawo Abuja gabanin Sallar La'asar, bisa bidiyon saukarsa da muka gani.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya saki bidiyon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel