Buhari ya lula Sokoto domin jajantawa wadanda 'yan ta'adda suka yi wa barna

Buhari ya lula Sokoto domin jajantawa wadanda 'yan ta'adda suka yi wa barna

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Zamfara domin yin ta'aziyyar mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren ta'addanci
  • Buhari zai yi ziyarar ne a yau Alhamis, 27 ga watan Janairu, bayan ya bar jihar Sokoto inda zai kaddamar da aiki
  • A kwanakin baya ne yan ta'adda suka kai farmaki kauyukan Zamfara inda suka halaka a kalla mutane 200

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Zamfara a yau Alhamis, 27 ga watan Janairu, domin jajantawa al'ummar jihar dangane da hare-haren ta'addanci da aka kai masu wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Tuni shugaban kasar ya bar fadar villa a safiyar nan zuwa jihar Sokoto inda zai kaddamar da wani sabon kamfanin siminti na tan miliyan uku da kamfanin BUA ya gina.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da wani katafaren kamfanin simintin BUA

Buhari ya lula Zamfara domin jajantawa wadanda 'yan ta'adda suka yi wa barna
Buhari ya lula Zamfara domin jajantawa wadanda 'yan ta'adda suka yi wa barna Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Buhari zai kuma kaddamar da tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 48 a jihar sannan sai ya wuce Zamfara domin ziyarar ta'aziyya.

Hadimin shugaban kasar a kafofin sadarwar zamani, Buhari Sallau ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a shafin nasa:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kasance a Sokoto a safiyar yau, don kaddamar da kamfanin simitin BUA na tan miliyan uku duk shekara a Sokoto da tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 48, kafin ya tafi Zamfara don yiwa mutane jaje kan hare-haren baya-bayan nan a yankunan jihar."

A kalla mutane 200 aka yi zargin yan bindiga sun kashe a kauyukan jihar a farkon wannan watan.

Zamu share yan bindiga daga doron ƙasa, Shugaba Buhari ya tabbatarwa gwamnan Sokoto

A wani labarin, mun ji cewa Shugaba Buhari, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na magance yan bindiga domin kare yan Najeriya daga sharrin su.

Kara karanta wannan

Mu ba jam'iyyar siyasa bace: ACF ta gargadi mambobinta wajen marawa dan takara baya

Buhari ya yi wannan furucin ne lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyarar jaje ga gwamna Aminu Tambuwal bisa kisan matafiya 23 a jihar Sokoto.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin gwamnan Sokoto, Muhammad Bello, ya fitar ranar Asabar, kamar yadda daily Nigerian ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel