Bayan dage zuwa Zamfara saboda bacin yanayi, Buhari ya dira Abuja

Bayan dage zuwa Zamfara saboda bacin yanayi, Buhari ya dira Abuja

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira birnin tarayya lafiya bayan ziyarar kaddamar da aiki a Sokoto
  • Shugaban kasan ya nufi zuwa Zamfara daga Sokoto amma aka samu mishkilar hazo
  • Shugaba Buhari ya yi alkawarin komawa makon gobe amma ba za'a ayyana ranar ba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira a babbar tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Sokoto don kaddamar da kamfanoni.

Buhari wanda ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnati ya dawo Abuja gabanin Sallar La'asar, bisa bidiyon saukarsa da muka gani.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya saki bidiyon.

Bayan dage zuwa Zamfara saboda bacin yanayi, Buhari ya koma Abuja
Bayan dage zuwa Zamfara saboda bacin yanayi, Buhari ya koma Abuja Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Daga Sokoto, Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau

Shugaban kasar da safiyar yau Alhamis ya tafi jihar Sokoto inda ya kaddamar da wani sabon kamfanin siminti na tan miliyan uku da kamfanin BUA ya gina.

Buhari ya kuma kaddamar da tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 48 a jihar.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar Gwamnan jihar Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal; Gwamnan bankin CBN, Mr Godwin Emefele; Shugaban kamfanin BUA, Alhaji AbdulSamad Rabi'u, Shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, dss.

Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau

Shugaba Muhammadu Buhari ya fasa zuwa jihar Zamfara sakamakon bacin yanayi a sararin samaniya.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa Shugaban kasan ya shirya tashi daga Sokoto amma ya fasa saboda lalacewar yanayi, riwayar DailyTrust.

Matawalle yace shugaban kasa ya kirasa a waya kuma yace ya tayashi baiwa al'ummar jihar hakuri.

Yace Shugaban kasa ya ce zai dage zuwansa zuwa makon gobe amma za'a sanar da ranar da aka zaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel