Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

  • Gwamna Ganduje na jihar Kano ya sake jaddada matsayarsa kan yanke hukunci mai tsauri ga makashin Hanifa Abubakar
  • Ya bayyana haka ne a gidan gwamnatin jihar Kano yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar a cikin makon nan
  • Gwamna Ganduje ya ce dole ne gwamnatin jihar Kano ta tsaya tsayin daka don tabbatar da adalci a lamarin

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nace cewa dole ne a hukunta wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, kamar yadda dokar kisa da garkuwa da mutane ta jihar ta tanada, The Nation ta ruwaito.

Gwamna Ganduje na cikin ‘yan Najeriya da dama da suka fusata da kisan karamar yarinya da malaminta Abdulmalik Mohammed Tanko mai shekaru 30 da haihuwa wanda shi ne mamallakin makarantarsu ya yi.

Kara karanta wannan

Bayan dage ziyarar Zamfara, Buhari ya shirya zuwa jihar Nasarawa wata mai kamawa

Mashekan Hanifa Abubakar
Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An gurfanar da Abdulmalik a gaban kotu bisa zargin kisan kai, biyo bayan ikirarin da ya yi na cewa ya yi amfani da gubar bera ne wajen kashe yarinyar, bayan ya karbi kudin fansa na N100,000 daga hannun iyayenta.

Ganduje, wanda ya ce yana jiran ya rattaba hannu kan hukuncin kisa akansa, a jiya ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa:

"Za a binciki makarantu sosai domin samun cikakken tsaro."

Ya kuma janye lasisin makarantar marigayin da wasu fusatattun matasa suka kona.

A cewar gwamna Ganduje yayin taron majalisar zartarwar jihar (SEC) a Africa House Kano:

"Dole ne a yi adalci a matsayin hukuncin kisan gillar da aka yi wa Hanifa Abubakar Abba - yarinya 'yar shekara biyar da malaminta ya kashe, wanda ya kamata ya kasance mai kula da ita.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

“Jihar za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an yi adalci a wannan lamarin. Za mu yi iya kokarinmu don ganin cewa an yi aikin a cikin dan gajeren lokaci mai yiwuwa.
“Ina kuma tabbatar wa duk wanda ya aikata laifin zai samu hukuncin da ya dace dashi a kan wannan danyen aikin da ya aikata."

Daily Post ta kawo cewa, Gwamnan ya kuma ce za a ci gaba da tantance makarantu a fadin jihar don tabbatar da amincin yara.

A cewarsa:

“Za a ci gaba da tantance makarantunmu don tabbatar da cewa suna da aminci. Muna son inganta kokarinmu na tabbatar da tsaron makarantunmu da yaranmu.
“Muna kuma yabawa jami’an tsaro bisa bin diddigin wanda ake zargi da kashe Hanifa. Gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin iya kokarinta wajen tabbatar da tsaron jihar Kano.”

An kamo matar makashin Hanifa, an kai ta kotu, amma ta musanta komai

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan Hanifa, an sake kashe wata yarinya a jihar Kano: Gwamna Ganduje

A wani labarin, Jamila Muhammad Sani, matar makashin Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5, ta gurfana a gaban babban kotun majistare na jihar Kano da ke zama a Gidan Murtala, Kano, bisa zargin hannu a boye Hanifa.

Jamila, ‘yar shekara 30, matar Abdulmalik Tanko ce, wanda ake shari’a kan tuhume-tuhume hudu da suka hada boye wacce aka yi garkuwa da ita, hada baki, garkuwa da dan mutum da kuma kisan kai.

Mai gabatar da kara, a yayin da take karantawa Jamila rahoton farko na bayanai, ta yi zargin cewa ta boye wacce aka sace a gidanta na tsawon kwanaki biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel