Buhari: Lamarin tsaro a arewa maso yamma yana matuƙar damu na

Buhari: Lamarin tsaro a arewa maso yamma yana matuƙar damu na

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana matukar damuwa da halin rashin tsaro a arewa maso yamma
  • Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi a fadar Sarkin Musulmi yayin ziyarar jaje a Sokoto
  • Buhari, ya ce gwamnatinsa ta bawa sojoji da sauran jami'an tsaro umurnin kada su sassauta wa duk wani ɗan ta'adda ko ɗan bindiga

Jihar Sokoto - Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi matukar damuwa da batun tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, The Cable ta ruwaito.

Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne yayin jawabinsa a fadar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar a Sokoto.

Buhari: Lamarin tsaro a arewa maso yamma yana matukar damu na
Shugaba Buhari ya ce lamarin tsaro a arewa maso yamma yana matukar damunsa. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsalolin tsaro, Buhari ya ba da tabbaci

Buhari ya ce yayin da tsaro a arewa maso gabas da kudu maso kudu ya inganta idan aka kwatanta da yadda ya ke lokacin da ya hau mulki, kallubalen a arewa maso yamma wani lamari ne daban.

Shugaban na Najeriya ya ce ya umurci sojoji da sauran hukumomin tsaro kada su sassauta wa duk wanda aka samu yana barazana ga tsaro da lafiya yan Najeriya, rahoton The Cable.

Buhari ya ce:

"A kullum, muna damuwa da abubuwan da ke faruwa a arewa maso yamma. A lokacin da muka zo, idan ƴan Najeriya za su mana adalci, sun san an samu cigaba a arewa maso gabas da kudu maso kudu, amma a gaskiya abin da ke faruwa a arewa maso yamma yana tada min hankali.
"Mutane daga wuri ɗaya, al'ada ɗaya, suna kashe juna, suna sace kayan juna. Za mu yi iya kokarin mu kuma an bawa sojoji da sauran hukumomin tsaro umurnin kada su raga wa duk wani ɗan bindiga ko ɗan ta'adda.

Kara karanta wannan

Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma

"Za mu mika kasa mai tsaro fiye da yadda muka gaje ta."

Shugaban kasar wanda ya yi wa jihar jaje bisa hare-haren da yan bindiga suka kai a baya-bayan nan ya ce 'Najeriya za ta yi nasara a yaƙin da ta ke yi a azzalumai'.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel