Jigawa: 'Yan sanda sun yi ram da wadanda ake zargi da halaka 'yan sanda 2

Jigawa: 'Yan sanda sun yi ram da wadanda ake zargi da halaka 'yan sanda 2

  • Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta damke miyagun da ake zargi da kashe 'yan sanda biyu a jihar
  • An kama 'yan ta'addan da bindigogi biyu da suka sace na 'yan sandan da suka kashe a karamar hukumar Taura ta jihar
  • An samu wannan nasarar ne bayan amfani da bayanan sirri da aka yi wurin kai samame maboyar 'yan ta'addan

Jigawa - Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta sanar da damke mambobin wata kungiyar 'yan daba da ake zargi da kisan 'yan sanda biyu, sace sirikin wani fitaccen da kasuwa da kuma aikata lamurran ta'addanci a yankin arewa maso yamma na jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi nasarar cafke wadannan miyagun ne bayan samamen da aka kai maboyar su da ke kauyukan Dajin Maizuwo, Dan Gwanki da Yandamo a karamar hukumar Sule Tankarkar ta jihar.

Kara karanta wannan

An kama tsohuwa yar shekara 80 da wata mata suna yunkurin garkuwa da mutane

Jigawa: 'Yan sanda sun yi ram da wadanda ake zargi da halaka 'yan sanda 2
Jigawa: 'Yan sanda sun yi ram da wadanda ake zargi da halaka 'yan sanda 2. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Aliyu Sule Tafida, yayin bayyana wadanda ake zargi a hedkwatar 'yan sandan da ke Dutse a ranar Alhamis, ya ce an yi wannan nasarar ne bayan rahotannin sirri da suka samu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mutum 14 da ake zargin sun hada da maza goma da kuma mata hudu. Akwai wasu wadanda ake zargi daga Kaduna da aka damke su da yara shida.

Kayayyakin da aka damke su da su sun hada da bindigogi uku, harsasai masu rai 308, bindigar harbo jirgi 1, kudi har N2 miliyan, adduna, wayoyi shida da batira 9, layikan waya 12 da mota kirar Toyota Hiace mai mazaunin mutum ashirin da takwas.

Daily Trust ta ruwaito yadda aka kashe 'yan sanda biyu, daya sifeta, daya kuma sufirtandan a yayin da suka yi arangama da wadanda suka sace sirikin Haruna Maifata, fitaccen dan kasuwa kuma dan kwangila a Jigawa.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Kwamishinan 'yan sanda ya ce biyu daga cikin bindigogin da aka samu daga wadanda ake zargin suna daga cikin wadanda miyagun suka sace daga 'yan sanda da suka kashe a kauyen Kwalam da ke karamar hukumar Taura ta jihar.

Sabon rikici ya barke a kudancin Kaduna, rayuka 6 sun salwanta

A wani labari na daban, makiyaya uku aka kashe a sassa daban-daban na Zangon Kataf da karamar hukumar Kauru da ke kudancin jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, reshen kudancin Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa Albarka, ya sanar da Daily Trust cewa, an tsinta gawar wani makiyayi mai suna Yusuf Mamuda mai shekara goma sha shida a ranar Lahadi a yankin Zaman Dabo da ke masarautar Atyap ta Zangon Kataf, kuma an cire kansa tare da tafiya da shi.

Ya ce an kashe wani mutum tare da dan uwan sa duk a Zangon Kataf din yayin da ya tsaya siyan fetur da babur din sa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da hatsabibin ɓarawo dauke da IPhones 16, kwamfuta da wasu kayayyaki a Oyo

Asali: Legit.ng

Online view pixel