Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

  • Jami'an tsaro na hadin gwiwa a jihar Neja sun kama masu laifi 28 a wani samame da binciken gida-gida da suka yi
  • Har ila yau dakarun tsaron sun kwato muggan makamai da layoyi iri-iri a wajen wadanda ake zargin
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 25 ga watan Janairu

Niger - Rundunar tsaron hadin gwiwa a jihar Neja sun kama masu laifi 28 sannan sun samo layuka iri-iri, kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta bayyana a ranar Talata, 25 ga watan Janairu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an gudanar da aikin na hadin gwiwa ne tsakanin jami'an soji, DSS, yan sanda, NSCDC da yan banga, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zamfara: An gurfanar da dillalin motocci kan zargin cin 'sassan jikin yaro' ɗan shekara 9

Ya ce dakarun sun kai wani gagarumin samame tare da binciken gida-gida a Unguwar-Biri da ke karamar hukumar Bosso a ranar 25 ga watan Janairu.

Yan sanda sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja
Yan sanda sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Aikin zai ci gaba da gudana domin tsamo duk wasu bata-gari har sai an raba birnin da miyagu. Kwamishinan yan sandan jihar Neja, CP Monday Bala Kuryas, ya gargadi duk masu tayar da zaune tsaye da su daina ko su hadu da fushin doka."
"Dukkan wadanda ake tuhuma suna karkashin bincike a SCID, Minna kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunta su da zarar an kammala bincike."

Abubuwan da aka kwato daga miyagun sun hada da kibiyoyi 10, adduna guda bakwai, wukake takwas, sanduna tara, bututun shisha biyar, abun yankan itace daya, gatari daya, sandar karfe daya, abun yankan karfe daya, almakashi daya.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bindige 'yan sanda har Lahira, sun yi awon gaba da babban ɗan kasuwa a Jigawa

Sauran kayayyakin sune sukun-direba guda biyu, wayoyin hannu 13, buhuna 17, ledoji tabar wiwi guda hudu, layoyi iri-iri da wasu tufafi da silifas, rahoton Daily Post.

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

A wani labarin,. 'Yan bindiga masu tarin yawa sun kai farmaki karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, a wannan karon sun sheke mutum 1 yayin da suka yi garkuwa da sauran mutanen kauyen guda 15, wadanda yawancin su mata ne.

Channels TV ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan kamar yadda aka bada labari sun kai farmaki kauyen Batagari a yankin Maikujeri na karamar hukumar, yayin da suka bayyana a kan babura.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, sun iso kauyen ne yayin da suka yi ta harbi a iska dan su jefa firgici a zukatan mazauna kauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel