Sabon rikici ya barke a kudancin Kaduna, rayuka 6 sun salwanta

Sabon rikici ya barke a kudancin Kaduna, rayuka 6 sun salwanta

  • Sabon rikici ya barke tsakanin makiyaya Fulani da wasu 'yan ta'adda da ke yankunan Kauru da Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Wasu miyagu sun kashe makiyayi inda suka tsinke kansa tare da awon gaba da shi, sauran makiyayan sun sha da kyar
  • Har ila yau, wasu miyagu da ake zargi sun kashe mai babur da dan uwansa tare da zuba wa shanu takwas guba inda suka yi mushe

Kaduna - Makiyaya uku aka kashe a sassa daban-daban na Zangon Kataf da karamar hukumar Kauru da ke kudancin jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, reshen kudancin Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa Albarka, ya sanar da Daily Trust cewa, an tsinta gawar wani makiyayi mai suna Yusuf Mamuda mai shekara goma sha shida a ranar Lahadi a yankin Zaman Dabo da ke masarautar Atyap ta Zangon Kataf, kuma an cire kansa tare da tafiya da shi.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Sabon rikici ya barke a kudancin Kaduna, rayuka 6 sun salwanta
Sabon rikici ya barke a kudancin Kaduna, rayuka 6 sun salwanta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce an kashe wani mutum tare da dan uwan sa duk a Zangon Kataf din yayin da ya tsaya siyan fetur da babur din sa.

Albarka ya ce an kara kashe wani makiyayi mai suna Amadu Surubu yayin da matasa da makamai suka kai farmaki kasuwar Bakin Kogi da ke karamar hukumar Kauru a ranar Litinin.

An kuma zargi cewa an saka wa wasu shanu takwas guba a yankin Fadama da ke karamar hukumar Kaurun inda suka yi mushe, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika, yayin jawabin shugaban matasan masarautar Atyap, Gabriel Joseph, ya ce maharan sun kutsa Kurmin Masara da ke masarautar a ranar 11 ga watan janairu inda suka kashe mutum uku tare da kone gida daya da motar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Labari ne mai ban tsoro - Dattawan arewa sun yi Allah wadai da kisan Hanifa

Sai dai kuma, kwamishinan al'amuran cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan, a wata takarda da ya fitar jiya ya tabbatar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu biyu suka jigata.

Ya ce an shiga tashin hankali a yankin tun bayan da miyagun suka cire kan makiyayin kuma suka tafi da kan shi, inda sauran makiyayan suka sha da kyar.

Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron kasa ta ce ta halaka 'yan ta'addan 49 a karkashin ayyukan sojojin ta yayin da 'yan ta'addan 863 suka mika makaman su a makonni biyu da suka gabata.

Daraktan yada labarai, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan yayin bayar da bayani kan ayyukan sojojin a ranar Alhamis a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Onyeuko ya ce sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun halaka 'yan ta'adda 37, sun cafke 17 tare da samo miyagun makamai 117.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel