Da dumi-dumi: Rikici ya barke a Legas, gwamnati ta dakatar da kungiyar sufuri ta NURTW

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a Legas, gwamnati ta dakatar da kungiyar sufuri ta NURTW

  • Gwamnatin jihar Legas ta dakatar da ayyukan kungiyar sufuri ta NURTW a wani yankin jihar bayan samun tashin hankali
  • An dakatar da ayyukan kungiyar ba tare da bayyana lokacin dawowarsu ba, inda gwamnati ta bayyana matakan da take bi
  • An samu barkewar rikici a yankin Eyin Eyo da ke jihar, lamarin da ya kai ga tsoma bakin gwamnati cikin gaggawa

Legas - A ranar Talata ne gwamnatin jihar Legas ta dakatar da ayyukan kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) a Eyin Eyo da ke Church Street da gadar Idumota a tsibirin Legas, Vanguard ta ruwaito.

Dakatarwar da ba a bayyana lokacin dage ta ba ta zama dole ne bayan tashin hankali da aka samu a yankunan.

Legas ta dakatar da motoci a NURTW
Da dumi-dumi: Rikici ya barke a Legas, gwamnati ta dakarar kungiyar sufuri ta NURTW | Hoto: infocus.com

Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin sufuri Oluwatoyin Fayinka ne ya sanar da dakatar da aikin kungiyar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ba zan yi jinkiri wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan makashin Hanifa Abubakar ba, Ganduje

Fayinka ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya kunshi NURTW da sauran kungiyoyin da ke alaka da haka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Don hana ci gaba da tashe-tashen hankulan, Fayinka ya bayyana cewa hukumar kula da tashoshi na jihar Legas za ta koma bakin aiki a Eyin Eyo.

Fayinka ya ci gaba da cewa, an umurci rundunar Rapid Response Squad (RRS), da ta tura motocin dakon kaya (APC) a kan gadar Idumota domin tabbattar da doka da oda.

Za kuma su aiwatar da dakatar da NURTW a yankin kuma a lokaci guda za su fatattaki yaran Oju Opake da ke kan hanyar Plaza kusa da titin Church.

Haka kuma an dakatar da ayyukan kungiyar sufuri a titin Church da John, musamman Keke Marwa da Mini Buses (Korope).

Fayinka ya kara da cewa, RRS tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar za su tabbatar da tsaron rayuka a yankin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: FG ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani

BBC Pidgin ta ruwaito Fayinka yana cewa:

"An sanya jami'an tsaron jihar su jajirce domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a tsibirin Legas da kewaye."

Kungiyar kwadugo NLC ta dakatar da gagarumar zanga-zangar da ta shirya a fadin Najeriya

A wani labarin, kungiyar kwadugo ta kasa (NLC) ta dakatar da gagarumar zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranar 27 ga watan Janairu, 2021.

Vanguard ta ruwaito cewa NLC ta shirya yin zanga-zangan ne domin nuna adawa da shirin gwamnatin tarayya na zare tallafin man Fetur.

Shugaban kungiyar NLC, Ayuba Waba, shi ne ya bayyana haka yayin da yake zanta wa da manema labarai a Labour House, Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel