Bayan Likitoci da Malaman Makaranta, Ma’aikatan kotu sun tafi yajin-aiki a Najeriya

Bayan Likitoci da Malaman Makaranta, Ma’aikatan kotu sun tafi yajin-aiki a Najeriya

- Ma’aikatan shari’a sun fara yajin-aiki a wasu manyan Kotun kasar nan

- Kungiyar JUSUN ta bayyana abin da ya sa ta shiga yajin-aikin a yau

- Ma’aikatan su na zargin cewa Gwamnonin Jihohi sun hana kotu sakat

Rahotanni daga Daily Trust da sauran jaridu su na tabbatar da cewa ma’aikatan shari’a sun shiga yajin-aiki, har an kai ga rufe kotu da-dama a Najeriya.

Shugaban kungiyar malaman shari’a na bangaren jihar Legas, Kehinde Shobowale Rahamon, ya bayyana abin da ya sa ma’aikatan su ka tafi yajin-aiki.

Mista Kehinde Shobowale Rahamon ya ce har yanzu doka ta 10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kai ba ta fara aiki ba har yanzu.

KU KARANTA: Albashin Ma'ikata ya fi karfinmu , dole mu gagara biya - Ganduje

Shobowale Rahamon yake cewa wannan dokar da ba ta fara aiki ba, ta jawo ma’aikatan shari’a sun koma neman kudin kula da kotu a wajen shugabanni.

“Idan ka duba kundin tsarin mulki da kyau, mu ba kamar sauran ma’aikatan gwamnatin tarayya ba ne, doka ta ba mu gata, amma shugabanni sun hana mu.”

“Wannan karo ko dai a sake mana mara, ko kuma a rufe kotu har sai baba ta gani.” Inji Shobowale Rahamon.

Wani lauya da ke Legas mai suna Bayo Akinlade ya ce lallai ya na tare da JUSUN wajen fafutukar ganin an ba malaman shari’a damar su rika cin gashin-kansu.

Bayan Likitoci da Malaman Makaranta, Ma’aikatan kotu sun tafi yajin-aiki a Najeriya
Alkalin Alkalai na kasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kwastam sun yi babba kuma, sun yi ram da tulin buhunan wiwi

Bayo Akinlade yake cewa: “Maganar a nan ita ce dole kungiyoyin NBA da JUSUN su hada-kai domin su yi maganin kabe-kaben da ake yi wa kotu."

A dalilin wannan yajin-aiki an yi fatali da wasu karan da ake yi a kotunan da ke garuruwan Kano, Legas da nufin gwamnoni su daina zaluntar ma’aikatan kotu.

Dazu kun ji cewa kungiyar malaman makarantun koyar da fasaha da ke aiki a Najeriya ta fara yajin aikin sai baba ta gani a ranar Talata 6 ga wantn Afrilun 2021.

Shugaban kungiyar malaman manyan makarantun watau ASUP, Anderson Ezeibe ya sanar da hakan a Abuja, a lokacin da ya yi magana da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel