Abdulsalami: Yadda na gyara tare da kimtsa Obasanjo bayan fitowa daga gidan yari

Abdulsalami: Yadda na gyara tare da kimtsa Obasanjo bayan fitowa daga gidan yari

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya sanar da irin rawar da ya taka wurin gyara tare da kimtsa Obasanjo
  • Ya sanar da yadda Obasanjo ya same shi bayan fitowa daga gidan yari kuma ya ce zai maka gwamnatin Najeriya a kotu kan cutar sa da ta yi
  • Ya ce ya taushe shi tare da ba shi hakuri, kuma ya yi masa alkawarin cewa zai yi masa duk taimakon da zai iya

Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, tsohon shugaban kasar Najeriya ya yi bayanin rawar da ya taka bayan an sako tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga gidan yari a 1998.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Obasanjo ya na daga cikin shugabannin da Janar Sani Abacha ya jefa gidan yari bayan ya hau mulki.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Abdulsalami: Yadda na gyara tare da kimtsa Obasanjo bayan fitowa daga gidan yari
Abdulsalami: Yadda na gyara tare da kimtsa Obasanjo bayan fitowa daga gidan yari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan mutuwar farar daya da Abacha ya yi a shekarar 1998, Abdulsalami ya karba ragamar mulkin kasar kuma ya sako wasu daga ciki har da Obasanjo.

A wata tattaunawa da Trust TV, dattijon ya sanar da yadda aka gyara tare da kimtsa Obasanjo da wasu har suka dawo suka girgije.

"Mun sako Obasanjo da wasu 'yan gidan fursuna kuma muka yi musu rangwame. To a lokacin da Obasanjo ya fito, ya zo ya ganni inda ya ce zai maka gwamnati a kotu.
"Na tambaye shi dalilin da yasa zai yi hakan, sai ya ce an gurgunta masa kasuwancin sa, an take masa hakkin sa, bai yi juyin mulki ba da sauran dalilan sa.
"Sai na ce masa, ranka shi dade ka yi hakuri, komai ya wuce. Ka gode wa Allah cewa ka na da rai, ka manta da wadannan abubuwan. Abubuwan da ka lissafo da zan iya yi maka, duk zan duba su, sai muka rabu a haka".

Kara karanta wannan

Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara

Da aka tambaye shi ko ya gyara Obasanjo bayan fitowar sa daga gidan yari, Abdulsalami ya ce, "Kamar yadda na yi wa sauran ba! Me ku ke nufi da gyara shi?
"Tabbas ba shi kadai ba, dukkan wadanda aka garkame a gidan yarin, mun yi kokarin kawo gyara a rayuwarsu tare da taimakon su."

Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola

A wani labari na daban, Janar Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban kasa, ya bayyana wasu abubuwa da suka faru bayan mutuwar Chief Moshood Kashimawo Olawole wanda aka fi sani da MKO Abiola.

Abiola, wanda gwamnatin Janar Sani Abacha ta tsare, ya rasu yayin da ya ke tsare, wata daya tak bayan mutuwar Abacha.

A wata tattaunawa da Trust TV, ta yi da Abdulsalami, wanda ya zama shugaban kasa a wancan lokacin, ya ce ya shiga matukar dimuwa bayan da ya ji mutuwar Abiola.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Na faɗa wa Obasanjo kada ya shiga siyasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel