Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola

Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola

Janar Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban kasa, ya bayyana wasu abubuwa da suka faru bayan mutuwar Chief Moshood Kashimawo Olawole wanda aka fi sani da MKO Abiola.

Abiola, wanda gwamnatin Janar Sani Abacha ta tsare, ya rasu yayin da ya ke tsare, wata daya tak bayan mutuwar Abacha.

Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola
Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata tattaunawa da Trust TV, ta yi da Abdulsalami, wanda ya zama shugaban kasa a wancan lokacin, ya ce ya shiga matukar dimuwa bayan da ya ji mutuwar Abiola.

Gwamnatin Abacha ce ta kama Abiola bayan ya bayyana kan sa a matsayin shugaban kasa duk da mulkin soja a lokacin ta ki bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 12 ga watan Yunin 1993.

IBB ya kafa gwamnatin rikon kwarya wanda marigayi Chief Ernest Shonekan ne ya jagoranta amma Abacha ya yi juyin mulki bayan wata uku.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga nan ne ya watsa Abiola da wasu shugabannin soja da na farar hula zuwa gidan yari, Daily Trust ta ruwaito.

Abdulsalami ya karba gwamnati bayan mutuwar Abacha kuma daga nan ya saki wadanda aka tsare.

A tattaunawa da Trust TV, Janar din mai ritaya ya sanar da rawar da Ambasada Babagana Kingibe ya taka wurin bayyana labarin mutuwar Abiola ga iyalansa.

"A yayin da Abiola ke tsare, ba ya ga likitan sa, na san babu wanda ake bari ya gan shi. A lokacin da na zama shugaban kasa, bayan tuntuba kuma da tattaunawa da Ambasada Babagana Kingibe, na bai wa iyalansa ranar da za su dinga zuwa ganin shi.
"Kafin ranar mutuwar Abiola, iyalan sa sun zo daga Abuja don ganin sa. Saboda wani dalili, an hana dukkan iyalan ganin sa a lokaci daya. Idan wasu sun gan shi, sai wasu su gan shi washegari. Sun gan shi kamar jiya, ni kuma wata tawaga daga US suka zo gani na sai na ce za su iya ganin sa. A ka'ida, da yammaci ne iyalan ke ganin sa, saboda na amince tawagar Amurkan ta gan shi, sauran iyalansa sai suka jira.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

“Toh, yayin da ya ke ganawa da tawagar Amurka ne ya fara ciwo kuma daga nan jami'an tsaro suka nemi likitoci. Bayan sun ga abun ya tsananta, sai aka kai shi asibiti. Tawagar Amurkan da ta likitocin ne suka kai shi asibiti. A nan kuma ya rasu.
“Shugaban dogarai na ya kira ni ya ce ya na da mummunan labari. Ya sanar da mutuwar Abiola. Na shiga dimuwa. Ya sanar da ni cewa ya na tare da 'yan Amurkan nan. A lokacin ina bariki, sai na koma Villa. Na ce a kai bakin Amurkan gida na sannan na tashi daga aiki na tafi gida.
“Babban tashin hankalin shi ne, ta yaya zan sanar da iyalan Abiola kuma ta ya zan sanar da duniya mutuwar Abiola? Dole ne in sake gode wa Ambasada Kingibe saboda shi na kira nace ya kawo iyalan Abiola. Bayan ya kawo su ne na sanar da su abinda ke faruwa.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

“Kamar yadda ku ka yi tsammani, sun fara kuka. Ba zan iya tuna wacece ba cikin matan, na rike ta tana kuka, sai Susan Rice ta ce ba aikin ka ba ne shugaban kasa, bari in taimaka. A haka ta rike ta har sai ta daina kuka sannan muka tsara yadda za mu sanar da duniya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel