Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara

Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara

Sojoji tare da taimakon 'yan sa kai a daren Asabar sun ceto wani dan siyasa da iyalansa bayan musayar wuta da suka yi da 'yan ta'addan inda aka kashe 'yan ta'adda masu yawa.

majiyoyi daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara, sun tabbatar wa da Premium Times cewa, an sace dan siyasa Aminu Adamu a gidan sa da ke kwatas din Mareri da ke birnin.

Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara
Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Adamu wanda aka fi sani da Papa, shi ne manajan daraktan hukumar sufuri ta jihar Zamfara kuma makusancin Gwamna Bello Matawalle.

Wani mazaunin yankin mai suna Zayyanu Muhammad, ya sanar da cewa 'yan ta'addan sun bayyana a babura inda kai tsaye suka tsinkayi kwatas din Mareri inda Adamu da iyalansa su ke.

Kara karanta wannan

Dan Allah ku taya ni da addu’ar samun lafiya, Olisa Metuh ya roki ‘yan Najeriya

"A gaskiya ba Papa suka je sacewa ba. Barista Hafiz Sufyan suka je sata amma ba ya gida. Wurin karfe 12 da rabi na dare ne kuma ko da suka shiga gidan Papa, sun dinga tambayar inda makwabcin sa Barista Hafizu ya ke, amma ya ce ba ya gari. Sun ce an tabbatar musu ya na gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daga nan suka dauke shi da iyalansa. Daga nan ne jama'ar yankin suka sanar da 'yan sa kai da ke babban titi wadanda suka fuskancin 'yan ta'addan," yace.

Muhammad ya kara da cewa, 'yan sa kan sun bi 'yan ta'addan har wajen kwatas din, lamarin da ya tirsasa su sakin matan dan siyasan biyu da yaransa amma suka tafi da shi.

Wata majiya wacce ke zama kusa da yankin mai suna Ashafa Sani, ya ce sun ji harbe-harben sojoji da 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

"Ina kallon fim wurin karfe 1 na dare yayin da na fara jin harbe-harbe. Abun akwai tsoro amma mun gode Allah tunda an ceto su," yace.

An harbi Dani da Adamu har sau biyu a kafa yayin arangamar kuma an mika su asibiti.

"Ina tunanin sojoji sun zo kuma a bayyane ya ke cewa sun fi karfin su, 'yan ta'addan sun yanke hukuncin kashe Papa saboda sun harbe sa sau biyu a kafa. Sojojin sun cece shi kuma sun kai shi asibiti. Na je asibitin da yammacin yau domin ganin halin da ya ke ciki, makwabci na ne," yace.

Muhammad ya ce an kashe 'yan bindiga masu yawa har da wata mata a ciki, Premium Times ta ruwaito.

"Gawawwakin su suna cibiyar lafiya ta tarayya a Gusau. Na ga gawawwakin kuma dukkansu matasa ne. An ce mana 'yan ta'adda biyu ne kacal suka tsere," ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar ragargazar ‘yan bindiga a sansanin su da ke Gwashi, karamar hukumar Bukkuyum da wasu bangarori na dajin Anka da ke jihar Zamfara inda suka amso shanaye da dama.

Gidan Talabijin din Channels ya tattaro bayanai a kan yadda ‘yan bindiga suka yi kawanya a dajin Gando inda sojin suka zagaye su suka halaka yawancin su.

Mazauna kauyakun da ke kusa sun bayyana suna shagulgula a kan nasarar da sojojin suka yi yayin karon su da ‘yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel