Mahaifiyar Ɗan Majalisa a Kano da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta Bayan Biyan Miliyan N40m

Mahaifiyar Ɗan Majalisa a Kano da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta Bayan Biyan Miliyan N40m

  • Mahaifiyar kakakin majalisar dokokin jihar Kano ta shaki iskar yanci daga masu garkuwa bayan biyan makudan kuɗi a matsayin fansa
  • Honirabul Ali Ɗanja, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar, yace maharan sun saki mahaifiyarsa a wata karamar hukuma dake Jigawa
  • Yace sun biya miliyan N40 a matsayin fansa kafin a sake ta, kuma ta kwashe kwanaki 13 a hannun su

Kano - Bayan shafe kwanaki 13 a hannun yan bindiga, mahaifiyar ɗan majaisar jihar Kano da aka yi garkuwa da ita, Hajiya Zainab, ta shaƙi iskar yanci

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Hajiya Zainab, ta kuɓuta ne ranar Talata, bayan biyan masu garkuwa da mutane zunzurutun kuɗi miliyan N40m a matsayin fansa.

Hajiya Zainab, mahaifiya ce ga Honorabul Isiyaku Ali Danja, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano
Mahaifiyar Ɗan Majalisa a Kano da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta Bayan Biyan Miliyan N40m Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

A ranar 12 ga watan Janairu, 2022, masu garkuwa suka sace Hajiya Zainab a dakin baccinta dake ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano.

Yaushe maharan suka sako ta?

Ɗan majalisan, wanda shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Kano a yanzu, shi ne ya tabbatar da sako mahaifiyar ta shi ga manema labarai ranar Talata.

Haka nan kuma ya bayyana cewa maharan sun sako ta ne bayan biyan su zunzurutun kuɗi naira miliyan N40m kuɗin fansa.

Ali Ɗanja ya ƙara da cewa yana kan hanyar zuwa wata ƙaramar hukuma a jihar Jigawa domin ɗakko mahaifiyarsa, inda masu garkuwan suka aje ta.

Premium Times ta rahoto shugaban majalisan yace:

"Masu garkuwa sun sako mahaifiyata bayan biyan miliyan N40m, yanzu haka ina kan hanya domin ɗakko ta a wata ƙaramar hukuma dake jihar Jigawa."

A wani labarin na daban kuma Malam Tanko, wanda ya sace Hanifa Abubakar kuma ya kashe ta da shinkafar ɓera ya faɗi firar da suka yi ta karshe kafin ta mutu

Shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary, Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe ɗalibarsa Hanifa Abubakar, ya bayyana hirarsu da ita bayan shayar da ita guba.

Tun da farko, Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Tanko ya bayyana cewa ya yi amfani da maganin ɓera na N100 wajen kashe yarinyar yar shekara 5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel