Fallasa: Yadda Ɗan Majalisar Katsina Ya Sace Naira Miliyan 32 Na Ayyukan Mazaɓarsa, ICPC

Fallasa: Yadda Ɗan Majalisar Katsina Ya Sace Naira Miliyan 32 Na Ayyukan Mazaɓarsa, ICPC

  • Hukamar yaki da rashawa da sauran laifuka masu kama da hakan, ICPC ta bayyana yadda dan majalisar tarayya na mazabar Katsina ta tsakiya ya yi wata gagarumar sata
  • ICPC ta fallasa yadda aka ware N32,056,347.89 don yin ayyukan ci gaba ga mazabar dan majalisar amma ya wawushe kudin kuma ya kalmashe su
  • Har ila yau hukumar ta bayyana yadda wani dan kwangila ya bar ginin azuzuwan makarantar firamare a Kano duk da an biya shi gaba daya kudaden da ya kamata

Katsina - Hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka masu kama da hakan, ICPC ta fallasa yadda wani Dan Majalisar Tarayya na Jihar Katsina ya tsere da N32,056,347.89 da aka ba shi musamman don ayyukan mazabarsa, Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar ta kara da bayyana yadda wani dan kwangila ya saki gine-ginen azuzuwan makarantar firamaren gwamnati wacce UBEC ta dauki nauyi a kauyen Tsebarawa da ke karkashin karamar hukumar Ajingi cikin Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Katsina: Yadda dan majalisa ya sace N32m na ayyukan mazabarsa, ICPC
Dan majalisar Jihar Katsina ya karkatar da Naira miliyan 32 na ayyukan mazabarsa, ICPC. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wadannan fallashe-fallashen sun biyo bayan wani bincike na mazabu wanda hukumar ICPC ta yi a karo na III na watanni hudun karshen shekarar 2021 don gano duk wasu masu ha’inci da kuma wawurar dukiyar al’umma.

Ba a samu sunayen ‘yan majalisar da ‘yan kwangilar ba

Dangane da rahotanni da hukumar ta samu sakamakon bin diddiki wanda ta gabatar wa Daily Trust, hukumar bata bayyana sunaye ba saboda yanzu haka an dakatar da dan majalisar amma za a san abin yi kuma yanzu haka ana kokarin amso dukiyar daga hannun mahandaman.

Kamar yadda takardar ta bayyana:

“Daya daga cikin binciken ya nuna yadda wasu ‘yan kwangila da kuma wasu ‘yan majalisa su ka yi ha’inci, yayin da dayan bangaren ya nuna yadda masu kulawa da kwangila su ka ki yin ayyukan su yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai zata kaddamar da bincike kan makamai 178,000 da suka yi batan dabo

“A wata kwangilar da UBEC ta bayar a watan Disamban 2020 wacce ta sa a kammala cikin makwanni uku na gine-ginen azuzuwan makarantar firamaren gwamnati a kauyen Tsebarawa a karamar hukumar Ajingi ta Jihar Kano wacce wani dan kwangila ya ki kammalawa duk da an biya shi.”

Akwai kwangilolin da masu kula da su suka sa hannu a matsayin an kammala su kuma ba hakan bane

Rahoton ya kara bayyana cewa:

“Akwai wata kwangila ta gini da kuma sanya littafai da kayan amfanin wani dakin karatu a mazabar Katsina ta tsakiya wanda aka sauya samfurin ginin inda aka mayar da shi wani na daban ba wanda aka sanya hannu a kai ba.
“Sannan wanda zai kula da ginin ya sa hannu tare da tabbatar da cewa an kammala ginin da komai wanda aka yi amfani da N49,973,052.”

Kudin da aka kiyasta zai isa a kammala ginin N17,916,704.11 ne, wanda hakan ya nuna gwamnati ta tafka asarar N32,056,347.89.

Kara karanta wannan

Babban Sarki a Najeriya ya shawarci Buhari ya dawo da shirin WAI, tare da zartar da hukuncin kisa ga 'yan ta'adda, matsafa da dillalan miyagun kwayoyi

Rahoton ya kuma nuna yadda wasu jami'an IPCR biyu da aka nada don sa ido kan kwangilar da aka yi wa lakabi da 'samar wa matasan Nguru kudin fara sana'a' suka zauna a ofisoshinsu suka rubuta rahoto mai kyau na cewa an kammala aikin da kyau alhalin karara ba haka lamarin ya ke ba.

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

A wani labarin, an kama wani mai aiki a wurin wankin mota a Kano, Abdullahi Sabo, saboda tsere wa da motar kwastoma da aka kawo masa wanki, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Daura, Jihar Katsina da motar na sata.

Mr Kiyawa ya ce, a ranar 30 ga watan Nuwamba, yan sanda sun samu korafi daga wata mazauniyar Badawa Quaters a Kano inda ta ce wani mai aiki a wurin wankin mota ya gudu masa da motarsa Honda Accord ta shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel