Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

  • Yan sanda a Katsina sun yi nasarar kama wani Abdullahi Sabo da motar wata mata da aka bashi wankin mota a Kano
  • An kama Sabo ne a jihar Katsina da motar kirar Honda Accord kirar 2017 a Daura inda ya tafi ya sayar da motar
  • Mai wurin wankin motoccin a Kano ya amsa cewa ya dauki Sabo aiki ne ba tare da ya san shi ba sosai kuma ya ci amanarsa

Kano - An kama wani mai aiki a wurin wankin mota a Kano, Abdullahi Sabo, saboda tsere wa da motar kwastoma da aka kawo masa wanki, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Daura, Jihar Katsina da motar na sata.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina
Mai wankin mota da aka kama ya saci mota a Kano ya gudu Katsina. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Kiyawa ya ce, a ranar 30 ga watan Nuwamba, yan sanda sun samu korafi daga wata mazauniyar Badawa Quaters a Kano inda ta ce wani mai aiki a wurin wankin mota ya gudu masa da motarsa Honda Accord ta shekarar 2017.

Yadda lamarin ya faru

"A ranar 30/11/2021 misalin karfe 2 na rana, wata mazauniyar Badawa Quaters, ta ce ta kai motar ta, Honda Accord 2017 Model, da kudin ta ya kai Miliyan Takwas da Dubu Dari Biyar (N8,500,000:00) wurin wankin mota a Maidile Quaters, Karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano.
"Da ta dawo, sai ta tarar cewa babu motar kuma babu wanda ta bawa wankin motar.
"Yayin bincike, mai wurin wankin motar ya yi ikirarin cewa ya dauki wani Abdullahi aiki ba tare da a san ko shi wanene ba. Ya kuma bar shi tare da motar saboda yarda, shi kuma ya yi awon gaba da motar," - Kiyawa.

Kara karanta wannan

Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko

Wanda ake zargin ya amsa cewa ya sace motar ne

A cewar Mr Kiyawa, wanda ake zargin ya amsa cewa tabbas ya ace motar ne daga wurin wankin motar a Kano inda aka dauke shi haya, sannan niyyarsa shine ya sayar da motar.

Mako Ɗaya Bayan Miƙa Rayuwarsu Ga Yesu, Matasa 2 Sun Kashe Fasto a Cikin Coci a Legas

A wani labarin, wasu sabbin tubabu sun kai wa wani fasto hari Babatude Dada na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) hari a garin FESTAC, da ke karamar hukumar Amuwo Odofin sun halaka shi.

The Punch ta ruwaito cewa an kashe faston ne a cikin cocin RCCG da ke 13 Road, 6th Avenue, FESTAC Town, a ranar Talata, 2 ga watan Disamba.

Sabbin tubabun biyu da aka ce sun kashe faston sun fara zuwa cocin ne a karon farko a ranar Lahadi da ta gabata.

Kara karanta wannan

An kama wani soja da budurwarsa ɗauke da harsashi fiye da 90 a Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel