Gaskiyar lamarin: Fadar shugaban kasa ta magantu kan jita-jitan murabus din ministar kudi

Gaskiyar lamarin: Fadar shugaban kasa ta magantu kan jita-jitan murabus din ministar kudi

  • Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya karyata batun cewa ministar kudi, Zainab Ahmed ta yi murabus
  • Ahmad ya bayyana a shafinsa na twitter cewa akwai jita-jita da ke yawo cewa ministar ta sauka daga kujerarta
  • Ya ce ya zanta da daya daga cikin hadimanta na kut-da-kut wanda ya tabbatar masa cewa babu gaskiya a zancen barinta aiki

Abuja - Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karyata rade-radin da ke yawo na cewa ministar kudi, Zainab Ahmed, ta yi murabus daga mukaminta.

Mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwar zamani, Bahir Ahmed, ne ya karyata jita-jitan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter a ranar Litinin, 24 ga watan Janairu.

Gaskiyar lamarin: Fadar shugaban kasa ta magantu kan jita-jitan murabus din ministar kudi
Gaskiyar lamarin: Fadar shugaban kasa ta magantu kan jita-jitan murabus din ministar kudi Hoto: Federal Ministry of Finance
Asali: Facebook

Hadimin shugaban kasar ya ce ya zanta da wani hadimin ministar wanda ya tabbatar masa da cewar 'ba gaskiya bane' batun murabus din nata.

Kara karanta wannan

Watanni bayan dakatar da ita, Hadiza Bala Usman ta ga shugaba Buhari

Ya rubuta a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Akwai wani jita-jitan da ke yawo cewa mai girma ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Misis Zainab Shamsuna Ahmad ta yi mutabus. "Jita-jitan ba gaskiya bane kwata-kwata", daya daga cikin hadiman ministar na kut-da-kut ya fada mani a wayar tarho."

Buhari yace min bai sa kowa kara farashin man fetur ba: Shugaban majalisa

A wani labarin, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai ba kowa umurnin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin gwamnati ba.

Ahmad Lawan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Talata, 18 ga Junairu, 2022, rahoton DailyTrust.

Yace yana farin cikin fadawa yan Najeriya cewa Buhari bai sa kowa cire tallafin mai ba.

Kara karanta wannan

Watan Yuni zamu yanke shawara kan kara farashin litan man fetur, Majalisar tattalin arzikin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel