Watan Yuni zamu yanke shawara kan kara farashin litan man fetur, Majalisar tattalin arzikin Najeriya

Watan Yuni zamu yanke shawara kan kara farashin litan man fetur, Majalisar tattalin arzikin Najeriya

  • Majalisar tattalin arzikin tarayya ta bayyana lokacin da gwamnati za ta yanke shawarar kara farashin man fetur
  • Mambobin majalisar sun ce an tanadi kudin biyan tallafin mai daga yanzu zuwa Yuni a kasafin kudin 2022
  • Saboda haka bayan watan Yuni, za'a yanke shawara ko a sake da wani kudi ko kuma a cire tallafin gaba daya

Majalisar tattalin arzikin Najeriya NEC, a ranar Alhamis ta bayyana cewa za ta yanke shawara kan lamarin cire tallafin mai a watan Yuni, lokacin da kudin da akayi tanadi ya kare.

NEC ta ce duk da cewa ta dade tana tattaunawa kan lamarin, har yanzu bata yanke shawara kai ba.

Majalisar dake karkashin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ta zanna ne a dakin taron fadar Aso Villa ranar Alhamis, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Majalisar tattalin arzikin Najeriya
Watan Yuni zamu yanke shawara kan kara farashin litan man fetur, Majalisar tattalin arzikin Najeriya Hoto

Bayan zaman, manema labarai sun bukaci sauraron yadda aka yi a bakin Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda ya bayyana cewa sun fahimci dalilin da yasa aka tanadi kudin biyan tallafin na watanni shida kadai.

Gwamna Sule yace ba za su yanke wani shawara ba sai bayan kudin da aka tanada a kasafin kudin 2022 ya kare a watan Yuni.

A kara farashin litan mai zuwa N302 nan da Febrairu, kwamitin El-Rufa'i ta bada shawara

A jiya kun ji cewa Majalisar NEC ta baiwa gwamnatin tarayya shawarar a kara farashin litan man fetur zuwa N302 nan da watan Febrairu 2022.

Wannan shawara na cikin jeringiyar shawarin da kwamitin NEC mai tattaunawa da kamfanin mai NNPC kan farashin man da ya kamata a sanya a Najeriya ta bada, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

Wannan kwamiti dake karkashin jagorancin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ta gabatar da shawarin.

A 2021, NEC karkashin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta nada kwamitin sakamakon rashin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel