Yanzu-yanzu: Buhari yace min bai sa kowa kara farashin man fetur ba: Shugaban majalisa

Yanzu-yanzu: Buhari yace min bai sa kowa kara farashin man fetur ba: Shugaban majalisa

  • Yayinda ake sauraron alkawarin da gwamnati tayi na kara farashin mai a sabuwar shekara, shugaba Buhari ya ce babu ruwansa
  • Shugaban majalisan dattawa ya bayyanawa yan Najeriya hakan bayan ganawa da Buhari yau
  • A cewarsa, manyan jami'an gwamnatin da suka ce za'a cire tallafi aikin kansu suke

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai ba kowa umurnin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin gwamnati ba.

Ahmad Lawan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Talata, 18 ga Junairu, 2022, rahoton DailyTrust.

Yace yana farin cikin fadawa yan Najeriya cewa Buhari bai sa kowa cire tallafin mai ba.

Shugaban majalisa da BUhari
Yanzu-yanzu: Buhari yace min bai sa kowa kara farashin man fetur ba: Shugaban majalisa Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Zaku tuna cewa a watan Oktoba, Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed ta sanar da cewa gwamnatin tarayya zata cire tallafin mai bayan rabin shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Buhari Ya Rasu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, za'a baiwa talakawan Najeriya milyan arba'in kudi dubu biyar-biyar matsayin kudin mota don rage radadin karin da farashin man zai yi.

Amma Ahmad Lawan yau yace:

"Ina son yan Najeriya su san abinda nazo tattaunawa da Shugaban kasa."
"Da yawa cikinmu mun damu da maganganu, zanga-zanga, da jama'ar mazabunmu ke yi na cewa gwamnatin tarayya zata cire tallafin man fetur."
"Ina farin cikin sanarwa yan Najeriya cewa shugaban kasa bai fadawa kowa a cire tallafin man fetur ba."

Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur Kungiyar kwadago

Kungiyar Kwadagon Najeriya NLC, ta lashi takobin cewa yan Najeriya ba zasu yarda da wani sabon karin farashin man fetur ma da sunan cire tallafin mai.

NLC ta yi kira ga ma'aikata da yan Najeriya su shirya zanga-zanga kan wannan abu da gwamnati ke shirin yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hadimin Buhari ya bayyana adawarsa ga tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa

Shugaban NLC, Ayuba Wabbab, ya bayyana hakan a jawabin sabon shekara da ya saki ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel