Hotuna: Bayan kashe 'yan uwan sarki, 'yan bindiga sun tayar da bam a coci a Taraba

Hotuna: Bayan kashe 'yan uwan sarki, 'yan bindiga sun tayar da bam a coci a Taraba

  • Abun fashewa ya tashi a cocin katolika na St. John’s College, Mutum-Biyu, hedkwatar yankin Gassol da ke jihar Taraba
  • Shugaban kwalejin Rev. Fr. Emmanuel Vershima Ikyaan, ya bayyana cewa bam din ya tashi ne da misalin karfe 7:20 na yammacin Lahadi, 23 ga watan Janairu amma ba a rasa rai ba
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, DSP Abdullahi Usman, ya tabbatar da harin

Taraba - Rahotanni sun kawo cewa wani bam da ake zargin tsagerun yan bindiga da dasawa a cocin katolika na St. John’s College, Mutum-Biyu, hedkwatar yankin Gassol da ke jihar Taraba ya tashi.

Hakan na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan yan ta'addan sun kashe yan uwan hakimin garin Wuro Bokki da ke karamar hukumar Gosso ta jihar su uku.

Bayan kashe 'yan uwan sarki, 'yan bindiga sun tayar da bam a coci a Taraba
Bayan kashe 'yan uwan sarki, 'yan bindiga sun tayar da bam a coci a Taraba Hoto: TarabaTruth and Fact
Asali: Facebook

Shugaban kwalejin Rev. Fr. Emmanuel Vershima Ikyaan, ya bayyana cewa bam din ya tashi ne da misalin karfe 7:20 na yammacin Lahadi, 23 ga watan Janairu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bindige 'yan sanda har Lahira, sun yi awon gaba da babban ɗan kasuwa a Jigawa

Ikyaan ya ce:

"Mun godewa Allah ba a rasa rai ba, amma an lalata cocin. Kimanin mintuna 10 bayan tashin bam din a makarantar, sai muka fara jin karar harbe-harbe a garin.
"Matasan da wasu dalibai suna gudanar da wani taro a cocin wanda shine kuma dakin taro na makarantar sannan sun bar wajen jim kadan kafin tashin bam din.
"Wannan haraba ce ta bauta kuma idan irin wadannan hari na faruwa a coci, ina mutane za su gudu su je?
"Ina kira ga yin bincike sosai domin gano wadanda suka kai harin da kuma hukunta su."

Punch ta kuma rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Taraba, DSP Abdullahi Usman, ya tabbatar da harin a hira da aka yi da shi ta wayar tarho.

Usman ya ce:

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

"Abun da ya faru shine cewa wasu masu garkuwa da mutane sun zo domin sace mamallakin wani gidan mai a garin, abun bakin ciki gare su, basu samu aiwatar da nufinsu ba.
"A kokarinsu na guduwa don tserewa fadawa tarko, sai suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
"A cikin haka ne suka jefa bam a cocin don haifar da tsoro domin su samu damar tserewa. Wannan bam ne ya tashi sannan ya lalata ginin cocin."

Filato: An shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka farmaki jama'a, suka kashe da dama

A gefe guda, mazauna kauyen Dung da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato sun shiga jimami bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani wurin da ake hakar ma’adinai, inda suka kashe mutane hudu, Channels Tv ta ruwaito.

‘Yan bindigar sun kai farmaki wurin hakar ma’adinan ne a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka harbe ma’aikatan har lahira, lamarin da ya tilastawa rundunar ‘yan sandan jihar ta tura karin jami’anta zuwa yankin.

Kara karanta wannan

Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Gabriel Ubah ya fitar ranar Lahadi, ya ce an tura dakarun ne domin dakile tabarbarewar doka da oda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel