Yanzu-Yanzu: JAMB ta sanar da lokacin da za a fara rajistar UTME da DE na 2022

Yanzu-Yanzu: JAMB ta sanar da lokacin da za a fara rajistar UTME da DE na 2022

  • A yau Litinin ne hukumar jarrabawa ta JAMB ta fitar da wata sanarwa mai bayyana lokutan da za a yi rajistar UTME da DE na 2022
  • Hakazalika, sanarwar ta kuma bayyana lokutan da za a fara jarrabawar gwaji ta Mock da UTME na shekarar
  • Sanarwar na zuwa ne yayin da dalibai ke ci gaba da jiran sanarwar lokutan rajista da jarrabawar ta 2022

Abuja - A ranar Litinin ne hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa ta bayyana cewa za a fara rajistar jarrabawar shiga manyan makarantu da jarrabawar shiga kai tsaye na DE a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar ta na mako-mako da Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar Dokta Fabian Benjamin ya fitar, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Za a fara rajistar rubuta JAMB
Yanzu-Yanzu: JAMB ta fadi lokacin da za a fara rajistar UTME na 2022 | Hoto: punchng.com
Asali: Depositphotos

A cewar rahoton The Nation, jadawalin abubuwan da za su faru inji sanarwar su ne:

"Za a fara rajistar UME/DE a ranar 12 ga Fabrairu 2022 kuma ta kare 19 ga Maris 2022. Za a yi jarrabawar gwaji ta Mock a ranar 20 ga Afrilu 2022. Jarrabawar UTME kuwa za a yi ta daga 20 zuwa 30 ga Afrilu 2022".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

JAMB ta kirkiro wasu sabbin darusa a manhajar jarrabawar UTME ta shekarar 2022

A wani labarin, hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta ce za ta gabatar da sabbin darussan kimiyya guda biyu a jarrabawar JAMB, Punch ta ruwaito.

Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka ranar Asabar 4 ga watan Disamba a Abuja. Darussan sune Physical Health Education da Computer Science.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Oloyede yace: "Muna tambaya da wayar da kan jama'a, musamman dalibai, wadanda za su yi jarrabawar, cewa wadannan darussa biyu na kimiyya ne da za a kara a zabinsu don fadada damar da masu rubuta jarrabawa zasu iya samun damar shiga manyan makarantu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel