'Yan sanda sun gano gawar yaro ɗan shekara 3 da ya ɓace a Jigawa

'Yan sanda sun gano gawar yaro ɗan shekara 3 da ya ɓace a Jigawa

  • Rundunar yan sandan Jihar Jigawa ta gano gawar wani yaro dan shekaru uku, Aminu Bukar, wanda ya bace kimanin sati daya da ya gabata
  • ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun yan sandan JIhar Jigawa ya ce an gano gawar ne a dajin Tudun Mai Jambo, kilomita daya daga kauyensu Aminu
  • Shiisu ya ce binciken da yan sandan suka yi ya nuna babu wani abin zargi game da mutuwar yaron, an kuma mika gawarsa ga yan uwansa bayan likita ya tabbatar da mutuwarsa

Jigawa - Yan sanda a Jihar Jigawa sun gano gawar wani yaro dan shekara uku, mai suna, Aminu Bukar, wanda ya bace a ranar 14 ga watan Janairu a karamar hukumar Guri na jihar, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan cikin sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a a Dutse, babban birnin jihar.

An gano gawar yaro ɗan shekara uku da ya ɓace a Jihar Jigawa
'Yan sanda sun gano gawar yaro dan shekaru 3 da ya bace a Jigawa. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shiisu ya ce mahaifin mamacin, Alhaji Bukar, tunda farko ya kai rahoton bacewar dansa misalin karfe 4 na yamma da kauyen Dolen Zugu a ranar, rahoton The Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shiisu ya ce bayan sun samu rahoton, tawagar yan sanda sun bazama sun fara aiki kuma daga bisani suka gano gawar Aminu a wani daji a Tudun Mai Jambo, kimanin kilomita daya daga kauyen.

Kakakin yan sandan ya ce an garzaya da Aminu zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Yan sanda sun ce babu zargin kashe shi aka yi

Ya ce binciken da 'yan sandan suka kammala ya nuna cewa babu wani abin zargi game da mutuwar yaron.

Kara karanta wannan

An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

Shiisu ya ce daga bisani an mika wa 'yan uwan yaron gawar domin su masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel