Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

  • Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi 111, Mai garin Lokoja ya yi garanbawul akan yin sha’ani da dare
  • Kamar yadda ya bayyana, ya hana duk wani sha’ani matsawar dare ya yi saboda tabbatar da tsaro
  • A cewarsa, bata gari su na amfani da wannan damar wurin cutar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba

Kogi - Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun kashe sojoji, sun raunata janar, sun yi awon gaba da motocin soji

Mai Garin Lokoja ya hana sha’ani da dare saboda harkokin kungiyoyin asiri
Mai Garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Akwai yankunan da miyagun su ka fi kai hari

‘Yan kungiyar asirin su kan kai farmaki bangarorin fadar sa da yankuna kamar Kabawa, Karaworo da kuma anguwannin da ke kusa da tsohuwar kasuwa.

Bisa ruwayar Daily Trust, basaraken ya bayar da umarni ga mabiyan sa don su tabbatar da umarnin na shi saboda kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a jihar.

Sarkin Warkan Wasa na Lokoja, Malam Muhammadu Baba Shata ya umarci duk wasu mawakan gargajiya da su yi kokarin bin doka don a zauna lafiya a cikin garin Lokoja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel