Da Dumi-Dumi: An bawa hammata iska tsakanin jami'an tsaron Buhari da na El-Rufai a Kaduna

Da Dumi-Dumi: An bawa hammata iska tsakanin jami'an tsaron Buhari da na El-Rufai a Kaduna

  • Jami'an tsaro a Jihar Kaduna sun samu sabani har ta kai ga cewa sun bawa hammata iska a yayin ziyarar Buhari
  • Rikicin ya samo asali ne a lokacin da wasu jami'an tsaro da ke tare da tawagar Buhari suka hana motar El-Rufai wucewa a gadar Kawo
  • A wannan lokacin, Gwamna Nasir El-Rufai yana tare da Shugaba Muhamadu Buhari a kan gadar saman Kawo domin a motoccin tawagar Buhari ya iso gadar

Kaduna - An shiga rudani a lokacin da jami'an tsaro suka rika bawa hammata iska tsakaninsu yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke kaddamar da gadan Kawo a tsakiyar birnin Kaduna, ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu Buhari yana Kaduna inda ya tafi domin kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi a Kafanchan, Zaria da Kaduna.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Da Dumi-Dumi: An bawa hammata iska tsakanin jami'an tsaron Buhari da na El-Rufai a Kaduna
Jami'an tsaro sun dambace tsakaninsu yayin ziyarar Buhari a Kaduna. Hoto: Gwamnatin Kaduna
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jim kadan bayan dawowarsa daga Kafanchan, Shugaban Kasar ya kaddamar da gadan Kawo.

Sai dai, cacan baki tsakanin jami'an tsaro da ke tare da shugaban kasa da wadanda ke Kaduna ya yi sanadin musayar naushe-naushe tsakaninsu.

Abin da ya haddasa rikicin tsakanin jami'an tsaro

Rikici ya samo asali ne bayan da jami'an DSS suka toshe gadan Kawo jim kadan bayan shugaban kasa ya hau gadan.

Gwamna Nasir El-Rufai, wanda da farko ya sauka daga motarsa, ya shiga mota cikin tawagar shugaban kasa zuwa gadan.

Jami'an tsaro, wadanda suka hana yan jarida da sauran manyan mutane hawa gadan na Kawo, sun tare hanya bayan El-Rufai da shugaban kasar sun hau kan gadar.

Amma, Mai tsaron El-Rufai, ADC, ya dage cewa sai an bari motar gwamnan ta wuce.

Daily Trust ruwaito cewa jami'an tsaron na shugaban kasa sun ki bude hanya, hakan ya janyo cece kuce har da musayar naushi.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

Daga bisani, an bari motar gwamnan ta wuce.

Buhari ya sauka a Kaduna bayan dawowa kai tsaye daga Gambiya

Tunda farko, kun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira a Jihar Kaduna domin ziyarar aiki na kwana biyu a Jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Ana sa ran zai kaddamar da wasu ayyuka da Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi.

Shugaban kasar ya iso Kaduna ne daga Banjul, Kasar Gambia, inda ya hallarci taron rantsar da Shugaba Adama Barrow, kan mulki karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel