Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya

Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya

  • Babbar kotun tarayya ta Abuja ta umurci hukumar tsaro ta DSS da kada ta sake gabatar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a gabansa sanye da tufafi daya
  • Mai shari'a Binta Nyako ce ta bayar da umurnin a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, bayan korafi da lauyan Kanu ya gabatar
  • Lauyan ya ce ana hana ma wanda yake karewa damar yin wasu abubuwan bukata a inda yake tsare

Abuja - Mai shari'a ta babbar kotun tarayya da ke Abuja, Binta Nyako, ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bari Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan awaren IPOB da ya sauya kayayyakinsa.

A baya, Nyako ta umurci DSS da ta bari shugaban na IPOB ya dunga yin wanka a duk lokacin da yake son canja tufafinsa, ya ci abinci yadda ya kamata da kuma gudanar da addininsa.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya
Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya Hoto: NTA Network News
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a zaman kotu na ranar Talata, 18 ga watan Janairu, Mike Ozekhome, lauyan Kanu, ya yi korafin cewa har yanzu wanda yake karewa baya samun kula mai kyau a hannun DSS.

Ya ce har yanzu Kanu na nan a kebataccen wuri kuma cewa duk wani da aka tsare idan ya gaishe shi sai shima a kebe shi a wuri daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jim kadan kafin ta dage zaman, Nyako ta tunatar da wanda ake kara cewa kurkuku ba katafaren wajen shakatawa bane.

Sai dai kuma, ta jadadda umurninta na baya cewa a bari shugaban na IPOB ya sakata ya wala yadda ya kamata, ciki harda sauya tufafin Fendi wanda ke jikinsa a lokacin da aka dawo da shi kasar a watan Yunin 2021, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Matar aure ta tsere da saurayinta ta bar mijinta da suka shafe shekaru 3 tare

Nyako ta kara da cewa:

"Bana so na kara ganinsa a cikin wadannan tufafin. Wannan har ya kusa kokewa. Sannan, ku tabbatar da cewar kun bar shi ya motsa jiki."

A halin da ake ciki, jaridar Punch ta rahoto cewa an dage sauraron shari'ar nasa zuwa ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.

Gwamnatin Buhari ta sake zayyano manyan laifuka kan Nnamdi Kanu

A baya mun ji cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume na ta’addanci a kan tsararren shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB; Nnamdi Kanu.

FG, a tsarin gyaran tuhumar da ta shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta kara yawan tuhume-tuhumen kan na farko da ta ke yiwa Nnamdi Kanu, Vanguard ta rahoto.

Shugaban kungiyar ta IPOB a baya yana fuskantar tuhume-tuhume bakwai na cin amanar kasa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Asali: Legit.ng

Online view pixel