Mijina ya kware wajen cizo, yana lakada mun duka idan ban yi Abinci ba, Mata ta nemi Kotu ta rushe auren

Mijina ya kware wajen cizo, yana lakada mun duka idan ban yi Abinci ba, Mata ta nemi Kotu ta rushe auren

  • Wata mata ta maka maigidanta a gaban kotu, ta nemi alkali ya datse igiyoyi uku na aurensa dake kanta nan take
  • Matar ta shaida wa kotu cewa mijinta yana zaluntar ta, ga cizo wani lokacin ya lakaɗa mata dukan tsiya idan ba ta yi abinci ba
  • Magidancin ya musanta zargin da mai ɗakinsa take yi a kansa, yace duk rikicin gidansa ita ke haddasa shi

Gombe - Kotun Majistire dake zamanta a Unguwar Idi, jihar Gombe, ta ɗage sauraron ƙarar da wata mata, Lawiza Mu'azu, ta shigar a gabanta, kamar yadda Punch ta rahoto.

Alkalin kotun, mai shari'a Garba Abdullahi, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, 2022, domin baiwa Lawiza damar gabatar da shaidunta.

Lawiza ta gurfanar da maigidanta, Alhaji Muazu, bisa zargin yana nana mata cizo a kowane lokaci suka samu wata matsala a tsakanin su.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ga APC: Mun gaji da gafara Sa, ku bai wa mata manyan mukamai

Kotun Majirtire
Mijina ya kware wajen cizo, yana lakada mun duka idan ban yi Abinci ba, Mata ta nemi Kotu ta rushe auren Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Matar ta kuma shaida wa kotun cewa mijin ta na lakaɗa mata dukan tsiya idan suka samu saɓani ko da bai taka kara ya karya ba.

This Day ta rahoto Matar tace:

"Rikicin mu na ƙarshe shi ne lokacin da naƙi yi mana abinci. Na yi haka ne saboda bai siyo icce ko gawayi ba. Da ya lakaɗa mun duka na farko, sai na tafi gida amma mahaifina yace na koma gidan mijina."
"Bayan dukan, sai mijina ya koma cizo na. Zai kama hannuna ya nana mun cizo idan ban yi abinci ba."

Saboda haka ta nemi kotu ta rushe aurenta da Muazu, domin a cewarta ba zata sake ɗaukar wannan cin mutuncin da yake mata ba.

Shin mijin ya amince da laifinsa?

Da yake martani kan zargin da matarsa ta masa, Muazu ya musanta maganar cizo da kuma dukan mai ɗakinsa Lawiza.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Mahaifiya ta wanke ɗiyar cikinta da tafasasshen ruwa kan aike

Ya shaida wa kotu cewa matan sa biyu, kuma Lawiza ta ƙi girki na tsawon mako ɗaya, wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar da muka yi cewa duk me girki ita zata ciyar da kowa a gidan.

Muazu ya ƙara da cewa sakamakon haka ita ma abokiyar zamanta ta hana ta abincin duk da ta girka.

"Hakan yasa ta fushi, ta kama ni tana neman wai na sauke hakki na, ta saka mun hannu a aljihiu zata ciro kuɗi, garin haka ne muka samu matsala, amma ni bana cizon ta."

A wani labarin na daban kuma Amarya da Ango sun rasa rayuwarsu lokaci daya makonni bayan baikon auren su

Wani saurayi da budurwarsa dake shirin zama Ango da Amarya sun rasa rayuwarsu lokaci ɗaya makonnin bayan amince wa zasu yi aure.

Masoyan biyu, Ma'aikatan jinya ne da suka yi aikin neman kwarewa a cibiyar lafiya ta tarayya dake jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Asali: Legit.ng

Online view pixel