Asiri Ya Tonu: An kama wani sojan Najeriya da ya yi shagali da miliyan N20m da aka tura asusunsa bisa kuskure

Asiri Ya Tonu: An kama wani sojan Najeriya da ya yi shagali da miliyan N20m da aka tura asusunsa bisa kuskure

  • Hukumar EFCC ta shigar da ƙarar wani sojan saman Najeriya gaban kotu bisa zargin amfani da kuɗin da aka tura masa bisa kuskure
  • Sojan wanda ke aiki a sansanin hukumar sojin sama dake Kaduna, ya fara amfani da miliyan N20m da suka shigo Asusun bankinsa
  • EFCC tace maimakon ya kai rahoto hukumarsu ko bankinsa, sai ya fara warware wasu matsalolinsa na rayuwa da kudin

Kaduna - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen Kaduna, ta gurfanar da sojan saman Najeriya a gaban kotu bisa satar miliyan N20m.

Rahoto ya nuna cewa, an shigar da ƙarar, Corporal Haruna Samuel, bisa tuhuma ɗaya, sata da amfani da kuɗi ba yadda ya dace ba.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Facebook, ranar Laraba.

Kara karanta wannan

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

Sojan sama
Asiri Ya Tonu: An kama wani sojan Najeriya da ya yi shagali da miliyan N20m da aka tura asusunsa bisa kuskure Hoto: EFCC FB Fage
Asali: Facebook

Me sojan ya yi da kuɗaɗen?

Hukumar yaƙi da cin hanci ta bayyana cewa Sojan, wanda yake aiki a sansanin rundunar sajojin sama dake Kaduna, ya samu saƙon shigowar kuɗi asusun bankinsa bisa kuskure.

A cewar EFCC, hukumar da ta ɗauke shi aiki ta tura masa miliyan N20m bisa kuskure, amma bai kai wa bankinsa rahoto ba kuma bai kai rahoto ofishin Akanta na sojojin sama ba.

Mamimakon haka sai ya shiga shagalinsa da kuɗin, inda ya magance wasu matsalolinsa cikinsu har da biyan bashi.

EFCC tace:

"Bisa kuskure aka tura masa kuɗin daga Asusun hukumar sojin sama. Duk da yasan baya tsammanin wasu kuɗi da suka kai haka, sojan sai ya zare wasu daga cikin kuɗin."
"Maimakon ya kai rahoton kuskuren sai ya fara harkokin gaban sa da kuɗaɗen, daga ciki har da biyan bashi."

Kara karanta wannan

Mijina yana cizo na, ya lakaɗa mun duka idan ban yi abinci ba, Mata ta nemi kotu ta raba auren

A wani labarin na daban kuma Gwamnan APC a Arewa ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yace babu tantama zai amsa kiran da yan Najeriya maza da mata, dake sassan duniya ke masa.

Bello, ya sanar wa masoyansa dake faɗin kasa cewa a halin yanzun ya maida hankali kan babban taron APC, amma da an kammala zai amsa kiran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel