Sabuwar doka: Sanatoci suna shirin kawo dokar da za ta hana karbar kudin hayan gida na shekara

Sabuwar doka: Sanatoci suna shirin kawo dokar da za ta hana karbar kudin hayan gida na shekara

  • Majalisar dattawa na shirin kawo dokar da za ta hana masu gidajen haya karbar kudin haya na shekara
  • Kamar yadda yake a kudirin wanda ya isa zauren majalisar domin yi masa karatun farko, masu haya za su biya kudin hayan farko na watanni uku, sannan su koma biya duk wata
  • Sanata Samart Adeyemi wanda ya dauki nauyin kudirin ya ce masu gidajen haya na matsawa mutane biyan kudin shekara daya ko biyu kuma ba kowa ke da karfin ba

Abuja - Mambobin majalisar dattawa sun gabatar da wani kudiri da ke neman a hana masu gidajen haya karbar kudin shekara daga masu yin haya.

Dokar na so a mayar da shi laifi ga masu gidajen haya su nemi kudin haya na gaba daga masu hayan gidaje, ofishoshi da filaye fiye da na watanni uku.

Kara karanta wannan

Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan

An gabatar da dokar ne domin yi masa karatun farko a yayin zaman majalisar na ranar Talata, 18 ga watan Janairu, gidan talbijin na Channels ta rahoto.

Sabuwar doka: Sanatoci suna shirin kawo dokar da za ta hana karbar kudin hayan gida na shekara
Sabuwar doka: Sanatoci suna shirin kawo dokar da za ta hana karbar kudin hayan gida na shekara Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Da yake jawabi ga yan jarida bayan zaman majalisar, wanda ya dauki nauyin kudirin, Sanata Samart Adeyemi, ya ce hakan zai ba masu hayan gida damar biyan kudin hayan farko na watanni uku a dunkule, sannan su biya sauran duk wata, rahoton Punch.

Ya ce masu gidajen haya na tursasa masu yin haya biyan kudin shekara daya ko biyu a dunkule kafin su basu hayan gidajensu kuma yan Najeriya da dama basu da karfin biyan haka.

Sanata Adeyemi ya kuma bayyana cewa wannan dokar da aka gabatar ta tanadi biyan kudin hayan watanni uku sannan bayan karewar kudin ana sa ran masu hayan za su koma biya duk wata.

Kara karanta wannan

Sanatocin jihar Katsina 2 sun yi watanni 25 a Abuja, ba su kawo korafi ko shawara 1 ba

Legit ta ji ra’ayoyin masu gidajen haya da masu haya kan sabuwar dokar

Wani mai bayar da hayan gidaje a garin Minna, Mallam Tanimu Ndanusa, ya ce kudi suke kashewa domin gida gidajen da suke ba mutane haya don haka kafa masu doka kan yadda za su yi da gidajen nasu kamar tauye su ne.

Ya ce:

"Kashe kudade muke domin mu gina gidaje. Yi mana wata ka'ida wajen ba da haya daidai yake da take hakkin mu na yin kasuwanci. Ba laifi bane a biya duk wata, amma ya ake fama da biya duk shekara balle wata-wata? Wasu ba za su biya na wata biyu sai su ba da na wata daya."

Wani mazaunin gidan haya da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce hakan zai saukaka masu matuka, kuma za su samu sauki a wajen yi kaura idan gida bai masu ba, don idan kudi ya shiga hannun masu gidan haya basa son biya.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

"Eh to, akwai sauki mutum ya biya haya na kankanin lokaci, saboda idan gida bai min ba zan iya kaura ba tare da yin asarar kudi masu yawa ba. Amma wasu masu bayar da hayan basa son biya."

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri kan halin da ake ciki a yanzu na tsadar kayan masarufi.

Buhari ya bayyana cewa yawan abincin da ake nomawa a kasar, musamman fadada noman shinkafa da aka yi, zai karyar da farashin kayan abinci, ta yadda kowa zai iya siyansa.

Shugaban kasar ya yi magana ne a bikin kaddamar da dalar shinkafa na Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Monoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a babban dakin baje kolin kasuwancin kasa da kasa na Abuja, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel