Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce gwamnatin sa tana ci gaba da bincike akan masu hada kai da ‘yan bindiga a jiharsa kuma za ta bayyana sunayen su
  • Matawalle ya yi wannan bayanin ne yayin tattaunawa da manema labarai na cikin gidan gwamnati bayan kammala wani taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Litinin
  • A cewarsa da zarar an tabbatar da su na da hannu za a yi gaggawar fallasa su kuma a gurfanar da su gaban kotu don yanke musu hukuncin da ya yi daidai da ayyukansu

Jihar Zamfara - Gwamnan Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatin sa ta na ci gaba da bincike akan masu hada kai da ‘yan bindiga don kawo cikas ga tsaro a jihar sa, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da sauran rina a kaba: Shekaru 6 da kawo TSA domin hana sata, har gobe ana tafka barna

Matawalle ya yi wannan bayanin ne ga manema labarai na cikin gidan gwamnati bayan kammala wani taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Litinin.

Zamfara: Matawalle ya bayyana shirin sa na bayyana sunayen masu hada kai da ‘yan bindigan jihar
Matawalle ya bayyana shirinsa na bayyana sunayen masu hada kai da ‘yan bindigan jihar. Hoto. Daily Trust
Asali: Facebook

A cewarsa za a fallasa sunayen su kowa ya ji

Kamar yadda ya ce:

“Mu na ci gaba da bincike akan masu hannu a ta’addanci kuma za mu yi gaggawar sanar da kowa da zarar bayanai sun tattaru a hannunmu. Mun zage damtse wurin yin aiki tukuru ne don kawo karshen rashin tsaro da kuma hukunta masu hannu a kai.
“Don haka da zarar an kammala bincike, za mu sanar da duniya gaskiyar abinda jami’an tsaro su ka gano a kai”.

Akwai masu rura wutar ta’addanci a jihar

A cewarsa, ba lallai a kawo karshen ta’addanci nan kusa ba saboda akwai masu rura wuta a karkashin kasa.

Kara karanta wannan

Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar

Ya kara da jaddada bayani inda yace mutane 58 kacal aka halaka a farmakin da ‘yan bindiga suka kai karamar hukumar Anka da Bukkuyum ba 200 ba.

The Punch ta ruwaito inda gwamnan yace duk da kokarin masu rura wutar na ganin ta’addanci ya hauhawa, jami’an tsaro suna ci gaba da samun nasarori a makwannin da suka gabata.

Ya kwatanta wannan nasarar da jajircewar shugaba Buhari ta hanyar tsananta tsaro inda yace ko a ranar Laraba an ga canji kwarai a jihar.

Matawalle ya bayyana yadda ya kai ziyara wuraren da aka kai farmaki kuma ya daura laifin ga ‘yan ta’addan siyasan da suke yada yawan mutanen da aka halaka su wuce gaskiyar yawansu.

Sarakunan Bungudu da na Anka ne suka sanar da shi mutane 58 kacal aka halaka ba 200 ba

A cewarsa:

“Saboda irin mutanen da mu ke da su a jihar Zamfara, bana tunanin ta’addanci zai yi saurin karewa don akwai wadanda ke da alhakin rura shi. Wasu suna amfani da damar ne.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

“Abinda kawai suke bukata shi ne su nuna wa ‘yan Najeriya cewa daga gwamnatin tarayya har jihar Zamfara ba su dauki harkar tsaro da muhimmanci ba. Duk da yadda muke kokari.”

Ya musanta yawan mutanen da ta’addanci ya shafa inda ya ce ya ga rahoto wasu suna yada cewa mutane 200 abin ya shafa, wasu 300 yayin da wasu suke cewa 500, amma daga shi har jami’an tsaro sun je wurin.

Kamar yadda ya ce:

“Da farko mun je Bungudu inda muka tambayi sarkin garin yace mutane 36 ne kacal ‘yan bindiga suka halaka bayan sun banka wa garuruwa biyu wuta. Sannan muka je Anka, inda sarkin ya ce mutane 22 suka halaka. Idan an tattara mutane 58 kenan.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel