Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki yan Najeriya da su kara hakuri kan yanayin da ake ciki a yanzu
  • Buhari ya ce saura kiris kayan abinci su yi araha a kasar domin ana nan ana fadada noman shinkafa da sauransu
  • Ya bayyana hakan ne a bikin kaddamar da dalar shinkafa na Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Monoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a Abuja

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri kan halin da ake ciki a yanzu na tsadar kayan masarufi.

Buhari ya bayyana cewa yawan abincin da ake nomawa a kasar, musamman fadada noman shinkafa da aka yi, zai karyar da farashin kayan abinci, ta yadda kowa zai iya siyansa.

Kara karanta wannan

Sunaye Da Hotuna: Baƙaƙen Fata 5 Da Suka Fi Kudi a Duniya

Shugaban kasar ya yi magana ne a bikin kaddamar da shirin dalar shinkafa na Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Monoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a babban dakin baje kolin kasuwancin kasa da kasa na Abuja, rahoton Leadership.

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya
Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya Hoto: Leadership
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa daga kakakin Shugaban kasa, Femi Adesina, shugaban kasar ya ce sama da manoma miliyan 4.8 suka samu tallafi daga shirin bayar da rance.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce anyi kari wajen samar da kayayyakin amfanin gona guda 23 da suka hada da masara, man ja, koko, auduga, rogo, tumatir da dabbobi.

Ya ce:

“A yau noman shinkafa a Najeriya ya karu zuwa metric tan miliyan 7.5 duk shekara. Kafin bullo da shirin bayar da tallafi, matsakaicin abun da ake samarwa a Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2015 ya kasance kasa da metric tan 4 duk shekara.

Kara karanta wannan

Kada ku kuskura ku zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni, Uwargidar Masari ta gargadi yan Katsina

“Ina sane da cewa buhuhunan shinkafa na tallafin za su dunga tafiya kai tsaye ne daga nan zuwa masana’antun sarrafa shinkafa a fadin kasar, wanda hakan zai kai ga masu sarrafa shinkafar su fitar da ita kasuwa. Matakin zai taimakawa kokarinmu wajen karyar da farashin shinkafa a Najeriya.
“Kafin wannan gwamnatin ta kaddamar da shirin bayar da tallafin, ingantattun masana’antun sarrafa shinkafa 15 ne kadai a Najeriya. A yau, muna da ingantattun masana’antun sarrafa shinkafa sama da 50 wanda ke samar da aiki da kuma rage yawan rashin ayyukan yi. Muna sanya ran karin ci gaba idan sabbin masana’antun sarrafa shinkafa biyu suka fara aiki a Lagas da Katsina.”

Tsadar Abinci: CBN Ta Kawo Mafita, Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya

A gefe guda, mun kawo a baya cewa a kokarinsu na samar da wadataccen abinci ga 'yan Najeriya tare da karya farashin shinkafa, CBN da Kungiyar RIFAN, sun fara batun kaddamar da sayar da tan miliyan tara na tallafin shinkafa ga masu sarrafata.

Kara karanta wannan

Shugaban BUA ya samu kusan rabin Tiriliyan a kwana 7 a lokacin da Dangote ya yi asara

Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele yayin da yake kaddamar da shirin sayarwar da kuma fara noman rani a Kaduna ya ce, bankin a shirye yake ko yaushe don tallafawa harkar noma, The Nation ta ruwaito.

Ahmed Mohammed na CBN reshen jihar wanda ya wakilci gwamnan, ya ce shirin an shirya shi ne don sayar da shinkafar a kan farashi mai rahusa da nufin karya farashin don amfanin kowa a Najeriya da ma wasu kasashen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel