Yanzu-Yanzu: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani katafaren gidan mai

Yanzu-Yanzu: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani katafaren gidan mai

  • Wani shahararren gidan mai a jihar Oyo ya kama da wuta da tsakar ranar yau Talata, inji rahotonnin da muke samu
  • An ce wutar ta kama ne a kusa da wata tankar mai da aka ajiye a cikin gidan man, an kuma yi asarar da yawa
  • Ya zuwa yanzu dai ba a samu cikakkun bayanai kan wannan mummunar gobara da ta tashi ba a yankin na Ibadan

Ibadan, Oyo - Shahararren gidan man da ke garin Ibadan a jihar Oyo, SAO, dake unguwar Falana, Challenge, Ibadan, a ranar Talata da yamma ya kama da wuta, Tribune ta rahoto.

Gobarar wadda ta tashi da tsakar rana ta tashi ne da wata tanka da aka ajiye a harabar gidan man, lamarin da ya yi sanadiyar konewar sassan tashar da dama.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

Taswirar jihar Oyo: Gobara ta tashi a wani katafaren gidan mai
Yanzu-Yanzu: Wani katafaren gidan mai ya kama da wuta a yankin Ibadan | Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ga jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Oyo sun isa wurin da lamarin ya faru kuma a halin yanzu suna ta faman kashe gobarar.

Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu a wani hatsarin da ya afku a garin Fidiwo dake jihar Ogun karshen babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Talata a lokacin da wata motar bas da ke dauke da kaya da ke kan hanyar zuwa Legas ta kutsa cikin wata tankar dizal.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Oyo ne suka tare tankar ta mai a lokacin da hatsarin ya afku.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

A wani labarin, Ibrahim Jubril, daya daga cikin iyayen da aka tsinci gawar ‘ya’yansu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a Legas, ya magantu kan wannan mummunan lamari.

Idan za a iya tunawa, an tsinci gawarwakin yara takwas da aka ce ‘yan shekara hudu zuwa shida ne a cikin wata mota da aka ajiye a kan titin Adelayo, Jah-Michael, a yankin Badagry a Legas, a ranar Asabar, 4 ga watan Disamba.

Da yake magana game da lamarin, Jubril wanda ya rasa ‘ya’ya hudu maza biyu mata biyu, ya ce babu wanda ya san yadda yaran suka shiga cikin motar, inji rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel