Jerin sunayen manyan yan bindigan da suka addabi al'ummar Zamfara

Jerin sunayen manyan yan bindigan da suka addabi al'ummar Zamfara

Wani Malamin Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto, Dr. Murtala A. Rufai ya bayyana sunayen kasurguman yan bindga da adadin mabiyansu.

Malamin ya bayyana hakan ne a littafin da ya wallafa mai suna 'Ni dan bindiga ne'.

A littafin, ya bayyana sunayen yan bindigan da kananan hukumomin da suka addaba

Ga jerinsu:

Karamar hukumar Muradun:

1. Sama’ila na Bayan Dutsi na da yara 150;

2. Jimmo Fadama na Bayan Ruwa na da yara 80;

3. Simoli Jaya na Bayan Ruwa na da yara 65 ;

4. Sahabi na Bayan Ruwa na da yara 250;

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

5. Na’akka na Bayan Ruwa na da yara 180 ;

6. Aminu Jajani na Bayan Ruwa na da yara 120 ;

7. Sani Ba ruwanka na Dagwarwa na da yara 135 ;

8. Uban Kafirai of Dagwarwa na da yara 250 ;

9. Mai bokolo na Dajin ‘Yar Tunniya na da yara 300 ;

10. Haruna Zango na Dammaka na da yara 280 ;

11. Muntari na Dudduɓi na da yara 31 ;

12. Ɓoyi na Dudduɗi na da yara 210 ;

13. Turji na Fakai na da yara 500 ;

14. Nakyalla na Filinga na da yara 213 ;

15. Najana na Gidan Bisa na da yara 96 ;

16. Sitanda na Gwari na da yara 156 ;

17. Dullu na Sububu na da yara 138 ;

18. Halilu Sububu na Sububu na da yara sama da 1,200 ;

19. Maiduna na Tankyalla na da yara 216 ;

Kara karanta wannan

Bayan rikici ya lafa a Filato, an sake hallaka Bayin Allah a wani danyen harin tsakar dare

20. Gwaska na Tungar Kolo na da yara 76 ;

21. Kabiru ‘Yankusa na Safrar Kaɗe na da yara 185 ;

22. Ƙaramin Gaye na Tungar Miya na da yara 242 ;

23. Ɗan Sa’adiya na Dagwarwa da Badako na da yara 48 ;

24. Ɗan Shehu na Kudo na da yara 140 ;

25. Mati na Kudo na da yara 165 ;

26. Ɗan Bello na Kudo na da yara 98 ;

Jerin sunayen manyan yan bindigan da suka addabi al'ummar Zamfara
Jerin sunayen manyan yan bindigan da suka addabi al'ummar Zamfara Hoto: Sheikh Ahmad Gumi
Asali: Twitter

ƊANSADAU

27. Ɗan Makaranta na north Madaka na da yara 460 ;

28. Dogo Gyaɗe na Dajin Babar Doka na da yara 2000 ;

29. Damana na Dajin na da yara 1500 ;

30. Ali Kacalla na Madada na da yara 1600 ;

31. Malam na yammacin Cebi na da yara 900;

32. Bulaki na gabashin ‘Yargaladima na da yara 1200 ;

33. Ciyaman na gabashin ‘Yargaladima na da yara 900 ;

34. Ɗahe na gabashin ‘Yar galadima na da yara 250 ;

Kara karanta wannan

Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo

35. Kawu na gabashin Ɗansadau na da yara 700;

36. Ado Lalo na gabashin Ɗansadau na da kimanin yara 350 ;

37. Bulak na gabashin Ceɓi na da yara kimanin 520 ;

38. Janburos na kudancin Madada na da yara 800 ;

39. Sani Bica na east Madaka has abna da yara out 180 ;

40. Ɗan Bagobiri na yammacin Ceɓi na da yara 230 ;

41. Nagala na yammacinMairairai na da yara 750 ;

42. Ali ƙanen Nagala na gabashin Mairairai na da yara 220 ;

43. Zahiru na Gandaya da Mairairai na da yara 175 ;

44. Mai Gariyo na kudancin Burwaye na da yara 56 ;

45. Yalo na kusa da Burwaye na da yara 85 ;

Karamar hukumar Zurmi

46. Kachalla na arewacin Mayasa hna da yara as 1200;

47. Maidaji na arewacin Labunde na da yara 1500;

48 Ɗanƙarami na Tsanu na da yara 750;

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: EFCC ta kwato N152bn da $386m daga mahandama a 2021

Karamar hukumar Birnin Magaji

50 Alhaji Zaki na Rugu na da yara 85 ;

51. Yalo na Rugu na da yara 60;

52. Hassan na Rugu na da yara 28;

53. Maidaji na Rugu na da yara 40 ;

54. Kachalla na Rugu na da yara 58 ;

Karamar hukumar Shinkafi

55. Atarwatse na Dajin Mashema na da yara 200 ;

56. Ɗan Maƙwado na Kamarawa da Bafarawa na da yara 550 ;

57. Nagona na Bafarawa da Surduƙu na da yara 200 ;

Karamar hukumar Tsafe

58. Idi na Guga na da yara 100 ;

59. Baba Yayi na Guga na da yara 100;

60. Juuli na Kwankwanba na da yara 100;

61. Tukur na Munhaye na da yara 90 ;

62. Alhaji Ado Aleru na Munhaye na da yara 2500;

63. Mabi na Munhaye na da yara 100;

64. Ɗan’ Ibiro na Munhaye na da yara 100;

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bola Tinubu ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na neman takara a 2023

65. Guntu na Munhaye na da yara 65;

66. Karki na Munhaye na da yara 70;

67. Lawali Bunka na Munhaye na da yara 80;

Wadanda ba'a san adadin yaransu ba

Shehu Bagewaye na Gusami ;

Dancaki odita na Zurmi LGA,

Standard & Sani black na Bingil,

Kabiru Maniya,

Malan ila,

Rageb,

Kacalla Haruna,

Katare,

Hasan da Husaini Jaja ona Gusau;

Dogo Hamza na Bukkuyum;

Auta na Anka

Yadda aka tattara sunayen

Malamin jami'ar ya tattaro wadannan sunaye ne daga mazauna unguwannin dake kusa da mabuyar yan bindigan.

Hakazalika yan kungiyar sa kai da aka tuntuba sun taimaka wajen tattara sunayen.

Wadanda aka sacewa yan uwa ma sun bada wasu sunaye da adadin mayakan.

Dr. Murtala A. Rufai yace:

"Duk da haka, wannan kawai hasashe mukayi. Muna da tabbacin sunayen shugabannin amma adadin yaransu na yawo ne basu zama waje guda."

Asali: Legit.ng

Online view pixel