Cikakken bayani: EFCC ta kwato N152bn da $386m daga mahandama a 2021

Cikakken bayani: EFCC ta kwato N152bn da $386m daga mahandama a 2021

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta ce ta samu nasarar kwace naira biliyan 152.09 da kuma dala miliyan 386.22 daga mahandama daban-daban a 2021
  • Wilson Uwujaren, shugaban fannin watsa labaran EFCC, ya bayyana hakan ta wata takarda da ya saki a Port Harcourt ranar Litinin
  • A cewarsa, hukumar ta amso pounds £1.182 miliyan da kuma miliyan 1.723 na Riyal din Saudi cikin wasu rikita-rikitar da ta auku a shekarar

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ta samu nasarar amso naira biliyan 152.09 da dala miliyan 386.22 daga mahandama da masu wawura daban-daban a shekarar 2021.

Wilson Uwujaren, shugaban yada labaran EFCC ne ya bayyana hakan ta wata takarda wacce ya saki a Port Harcourt ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kamaru ta lallasa Burkina Faso a wasan farko na gasar AFCON 2021

Cikakken bayani: EFCC ta kwato N152bn da $386m daga mahandama a 2021
Cikakken bayani: EFCC ta kwato N152bn da $386m daga mahandama a 2021. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, hukumar ta yaki da rashawa ta ce ta amso £1.182 miliyan Pounds da 1.723 miliyan na Saudi Riyal cikin shekarar.

“Sauran kudaden da aka amso sun hada da €156,246, 1,900 na Rand din Afirka ta kudu da 1,400 na dakar kasar Canada tsakanin Janairu zuwa Disamban 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ta amso wasu makudan kudade na Bitcoin da 0.08012 Mr Ethereum,” a cewarsa.

Mr Uwujaren ya kara da cewa, hedkwatar EFCC da ke Abuja ta bayyana batun amso wata naira biliyan 67,250, dala miliyan 375.66 da £1.152 miliyan pounds.

“Daga nan sai kuma ofishin EFCC na Legas da ya samu nasarar amso naira biliyan 70.316, dala miliyan 9.286 da £21,500 pounds.
“Ofishin hukumar na jihar Kaduna kuwa ne na uku a bambaro kudade, inda ya samu nasarar amso naira biliyan 3.339.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: SERAP ta maka Lawan, Gbajabiamila a gaban kotu kan bata biliyan N4.1bn

“Ofishin yaki da rashawa na Ibadan ya zo daidai da na Kaduna bayan amso dala 387,385,” kamar yadda yace.

Mr Uwujaren ya yanko inda shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa ya ce, duk kudaden da ake amsowa na gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi, na kananun hukumomi da sauran kamfanoni da sauran mutane.

Mr Bawa ya yaba wa hukumar da ma’aikatan ta akan jajircewarsu, ya kuma bukaci su kara nunka kokarinsu a shekarar 2022.

Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi

A wani labari na daban, an cigaba da shari'ar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Saminu Turaki a babbar kotun tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, bayan shekaru goma sha hudu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Turaki ya bayyana a gaban kotun a ranar 7 ga watan Disamba inda ya ke fuskantar zargi 32 kan wawurar wasu kudi da suka kai N36 biliyan.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An kashe 'yan Boko Haram 950, 24,059 sun mika wuya a kasa da watanni 7

A shekarar 2007, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta damke tshon gwamnan kuma ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai shari'a Binta Murtala Nyako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel