Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

  • Jagoran APC na kasa, Bola Tinubu ya bugi kirjin cewa zai shawo kan duk wasu matsaloli da ke gabansa don yin nasara a zaben shugaban kasa na 2023
  • Tinubu ya ce yana da yakinin zai yi nasara a zaben saboda gagarumin goyon bayan da yake da shi daga mutane
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo

Oyo - Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya ce da gagarumin goyon bayan jama’a, zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, lokacin da ya ziyarci gidan tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja na Ibadan, jaridar The Cable ta rahoto.

Tsohon gwamnan na Lagas ya bayyana a ranar 10 ga watan Janairu, cewa ya sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa na takarar kujerar shugaban kasa.

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu
Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Dan siyasar ya ce ya samu martani masu dadi daga manyan masu ruwa da tsaki kan kudirinsa na takarar shugaban kasa, rahoton Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jagoran na APC ya ziyarci Ibadan don yiwa gwamnan jihar, Seyi Makinde ta’aziyyar mutuwar Jimoh Oyewumi, Soun na Ogbomoso; Saliu Adetinji, Olubadan na Ibadan da Adebayo Alao-Akala, tsohon gwamnan Oyo.

Da yake magana bayan wata ganawa da Ladoja, Tinubu ya ce yana sane da kalubalen da ke gaba, amma ya nuna yakinin cewa zai zamo mai nasara.

Ya ce:

“Rayuwa kalubale ne kuma dole ka shirya tunkarar matsaloli da magance su. Ina da karfin gwiwar cewa zan shawo kan kowani irin kalubale. Na tabbata na fuskanci kalubale kuma ina da karfin gwiwar cewa zan shawo kansu.

“Martanin masu ruwa da tsaki game da kudirin takarar shugaban kasa na ya kasance mai kyau, mai karfafa gwiwa da dadi kuma wannan ya karfafa mani gwiwar cewa za mu yi nasara sannan mu lashe zaben.

“Rayuwa kanta kalubale ce kuma ina da karfin gwiwa da karfin ikon magance kalubalen. Muna duba zuwa gaba da gagarumin goyon bayan al’umman Najeriya, Za mu cimma gagarumin nasara.”

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

A gefe guda, mun ji cewa bayan ya ayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), babban jigon jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya samu karbuwa a wajen wasu yan Najeriya.

A yanzu haka akwai wasu mutane da suka nuna ra'ayinsu na son siyar hularsa da ta shiga kasuwar intanet. Ana dai tallata hulunan ne a dandamalin sadarwa ta Twitter.

Wani mai amfani da dandamalin na Twitter @Jbmomoh, ya fada ma mabiyansa cewa yana da wasu huluna na siyarwa. Wadannan huluna ba kowanne bane face kwafin hular al'ada da tsohon gwamnan na jihar Lagas ke sanyawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel