'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

  • Gwamnonin jihohin Zamfara da na Borno sun koka kan yadda 'yan ta'adda ke wuce gona da iri a cikin jihohinsu
  • Gwamnonin sun koka kan yadda aka samu sama da mutane 600,000 suka zama 'yan gudun hijira, lamari ne mai firgitarwa a cewar su
  • Zulum ya sanar da cewa, har yanzu 'yan ta'adda na rike da kananan hukumomi biyu a jiharsa kuma suna tare hanya tare da karbar haraji

Borno da Zamfara - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da takwaransa na jihar Zamfara, Bello Matawalle, sun koka akan yadda 'yan ta'adda suke cin karensu babu babbaka a jihohinsu.

Yayin da Zulum yace mayakan ISWAP za su fi tada hankula fiye da Boko Haram ba a Borno kawai ba, har da sauran bangarorin kasar nan idan ba'a kawo karshensu ba, Matawalle ya ce 'yan bindiga da dama ana sakinsu ba tare da mika su gaban kotunan shari'a don a yanke musu hukuncin da ya dace ba, hakan yasa sama da mutane 600,000 suka zama 'yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Zulum: Mayakan ISWAP sun fi na Boko Haram makamai, dole ne a dakile su

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka
'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan jihar Borno yayi jawabi yayin tarbar kwamitin majalisar dattawa akan al'amuran sojoji a Maiduguri, yayin da Matawalle ya karba tawagar gwamnatin tarayya da ta kai masa ziyarar jaje a Zamfara kan rasin da aka yi na Anka da Bukkuyum a jihar.

Gwamna Zulum yayin tattaunawa da kwamitin majalisar dattawa akan harkar tsaro, a gidan gwamnatin da ke Maiduguri a ranar Laraba, ya ce Boko Haram suna cin karensu babu babbaka a karamar hukumar Abadam da Guzamala.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan Boko Haram suke cin karensu babu babbaka a kananan hukumomi a Borno inda suke fuskantar barnar Boko Haram na tsawon shekaru.

A yayin da gwamnatin tarayya ta ke cigaba da fadin babu bangare a Najeriya da ya ke karkashin ayyukan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

Idan za'a tuna a lokaci daya, 'yan ta'addan yankin chadi sun kai hari Abadam da wasu birane kuma suka zauna tsawon watanni kafin su bar kasar Najeriya su cigaba da addabar 'yan ta'addan kasar Chadi.

Amma bayan 'yan ta'addan sun aje makamansu, Najeriya ta janye dakarun ta, ba a dade ba mayakan ISWAP suka kai hari birane da kauyuka a Abadam da Guzamala da sauransu.

Tun wannan lokacin, 'yan ta'adda ne ke mulkar kananan hukumomin wanda ba za su bar zaman lafiya a wurare da sansanin 'yan gudun hijara ba.

Mazauna yankin sun cigaba da biyan haraji ga hatsabiban don a barsu su koma gonakin su da kasuwanni, Daily Trust ta ruwaito.

Zulum ya bayyana damuwarsa a kan yadda mayakan ISWAP su ke kara yawa a yankin kudancin jihar bayan wartakar mabiyan marigayi Abubakar Shekau.

"Duk da na jinjina wa dakarun sojin Najeriya na samar da zaman lafiya da suka yi a yankuna daban-daban a fadin jihar, ina so in janyo hankalin sojojin da su yi yaki da ta'addanci kuma su fatattaki mayakan ISWAP wadanda a halin yanzu su ke tattara mayaka a wasu bangaren jihar," a cewarsa

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun kwace wasu kananan Hukumomi a Borno, Gwamna Zulum

"Idan ba'a dauki tsatstsauran mataki a kan karuwar yawan mayakan ISWAP ba, wadanda su ka fi gogewa, su ka fi mallakar kayan yaki, su ka fi hatsari, su ka fi kwarewa kuma su ka fi samun kudi fiye da Boko Haram, zai zama annoba ba ga jihar Borno kawai ba harda kasa baki daya.
"Su na kara yawa a kullum amma ba abu mai wahala bane a wurin mu shawo kan matsalolin ba; akwai bukatar mu wartaki ISWAP tun da wuri.
"Mayakan ISWAP suna tsayawa matsayar binciken sojoji tsakanin Damboa da Biu, suna amsar haraji daga yankunan," yace,

Asali: Legit.ng

Online view pixel