Yanzu yan bindiga maza suke kashewa a Zamfara, In ji Gumi

Yanzu yan bindiga maza suke kashewa a Zamfara, In ji Gumi

  • Suleiman Gumi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gummi da Bukkuyum a majalisar tarayya ya koka akan harin da ‘yan bindiga suka kai Bukkuyum inda yace maza suke halakawa
  • A cewarsa, sai sun tabbatar da cewa jinsin mutum namiji ne kafin su halaka shi kuma babu babba babu yaro kamar yadda ya shaida wa manema labarai a majalisar tarayya da ke Abuja
  • Dama a halin yanzu ‘yan bindigan sun tasa wasu jihohi na arewa maso yamma da arewa ta tsakiya gaba da garkuwa da mutane, kashe-kashe da sauran ayyuka na ta’addanci

Zamfara - Suleiman Gumi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gummi da Bukkuyum a majalisar wakilai ta tarayya ya koka akan yadda ‘yan bindiga suka tasa maza da kisa a ‘yan kwanakin nan, Premium Times ta ruwaito.

Gumi ya nuna rashin jin dadin sa akan harin kwanan nan da ‘yan bindiga suka kai Bukkuyum inda yace sai sun tabbatar da jinsin mutum sannan su halaka shi.

Zamfara: Yanzu yan bindiga maza su ke halakawa, Dan Majalisar Tarayya
Dan Majalisar Tarayya, Suleiman Gumi ya ce yanzu yan bindiga maza suke kashewa a Zamfara
Asali: Twitter

Dan majalisar ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Litinin a majalisar tarayya da ke Abuja.

Yadda ta’addanci ke kara hauhawa

A cikin shekaru kadan da suka gabata, yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na fama da hare-hare, kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran harkokin ta’addanci.

Bayan share watanni ana kai komo, a makon da ya gabata gwamnatin tarayya ta kira ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Kwana biyu da aukuwar hakan suka kai farmaki karamar hukumar Anka da Bukkuyum da ke jihar Zamfara inda suka halaka mutane 200.

Gwamnatin tarayya da ta jiha ta dauki matakai iri-iri ciki har da datse kafafen sadarwa da kuma karhanta sayar da man fetur a wasu wurare duk don kawo karshen ta’addancin.

Duk da daukan matakan nan, hare-haren basu kare ba

A ranar Litinin gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana yadda masu kai wa ‘yan bindiga bayanai suke kawo cikas akan ayyukan gwamnatin na kawo gyara a harkar tsaro a yankin.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka tura wa garuruwa 9 da ke karkashin karamar hukumar Bukkuyum wasika akan ko dai su biya haraji ko kuma su kai musu farmaki.

Yanzu maza suke kai wa hari

Gumi ya ce yanzu haka ‘yan bindigan sun tasa maza gaba kuma akwai yuwuwar tun da gwamnatin ta kira ‘yan bindigan da ‘yan ta’adda ne suka fara daukar wannan matakin.

Don haka ya yi kira ga sojoji akan lura da kuma kirkirar nasu dabarun don kawo mafita akan wannan matsalar.

Kamar yadda ya shaida:

“Yanzu maza ‘yan bindiga suke kai wa farmaki, kuma babu babba babu yaro. Sai sun duba sun tabbatar namiji ne yaro kafin su janyo shi su halaka.
“Maza suke nema yayin da mata suke tserewa. Canji a salon nasu yana isar mana da wani sako ne.
“Ina da tabbacin hakan ya na da alaka da kiran su da ‘yan ta’addan da gwamnati ta yi. Saboda idan ka kira mutum da dan ta’adda hakan na nufin zaka sauya naka salon na yaki da shi. Don haka yanzu dai muna jiran a sauya salon yakar su.”

Ya yaba wa Gwamna Matawalle a kan kokarin sa

Dan majalisar ya yaba wa gwamna Matawalle akan tuntubar jamhuriyar Nijar da ya yi. Inda yace wannan salo ne na datse hanyar da suke samun makamai.

A cewarsa tunda sojoji suna kokarinsu kuma ba ko ina ‘yan sanda zasu iya zuwa ba, ya kamata a samar da ‘Yan Sa kai ta ko ina kuma a basu makamai masu kyau don yaki da ta’addancin da ya addabi kowa.

An bindige sufetan 'yan sanda har lahira a cikin caji ofis

A wani labarin, an bindige wani dan sanda mai mukamin sufeta a caji ofis da ke Mgbidi a hedkwatar rundunar da ke Jihar Imo.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe dan sandan ne a lokacin da yan bindiga suka kai hari a daren ranar Juma'a.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da harin amma ya ce an fatattaki yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel