Mai laifi ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa

Mai laifi ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa

- Yan sanda sun kama wani mutumi da ya kashe budurwarsa don kudin fansa a jihar Osun

- A cewar hukumar tsaro, wanda ake zargin yak ware wajen siyar da sassan jikin dan adam

- Kwamishinan yan sandan jihar ya ce ana kokari don ganin an kama sauran mutanen

Wani mutum mai shekaru 31 a jihar Ogun, Tajudeen Monsuru ya tona cewa shi ya kashe budurwarsa, Mutiyat Alani don kudin asiri.

A wata hira da jaridar Daily Trust, Tajudeen ya ce ya shake budurwar har lahira a ranar da ta zo gidansa sannan ya yanke kanta don yin asirin kudi.

Ya ce yan uwan budurwar basu san cewa ta kai ziyara gidansa ba sannan cewa babu wanda ya zarge shi a lokacin da ake neman ta.

Mai laifi ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa
Mai laifi ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Iyayen budurwar sun kai karar lamarin zuwa hedkwatar yan sanda a Iwo cikin shekarar da ta gabata sannan aka kaddamar da batan marigayiyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Za mu kawo karshen yaki da ta'addanci a wannan shekarar, Buhari ya kaddamar

An tura lamarin zuwa ga sashin bincike na sirri a hedkwatar yan sanda da ke Osogbo, babbar birnin jihar don yin bincike.

Kwamishinan yan sanda a jihar, CP Wale Olokode ya ce an kama wanda ake zargin ne ta binciken sirri.

Olokode ya ce wanda ake zargin ya kuma kashe wani Akinloye Ibrahim da wasu da dama don kudin fansa.

Ya ce wanda ake zargin ya kuma kware wajen siyar wa da matsafa sassan jikin dan adam.

Wanda ake zargin ya yi bayanin cewa kisan budurwarsa ne ya fallasa shi saboda ya dauki wayanta sannan ya siyarwa wani.

Tajudeen ya bayyana cewa ya siyar da wayar marigayiyar budurwarsa kan N2,000 sannan cewa yan sanda sun bibiyi wayan tare da kama wanda ya siyi wayan lamarin da yayi sanadiyar da yan sanda suka kama shi.

KU KARANTA KUMA: Hanan Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya

Yan sanda sun hako gawar matar da na sauran mutanen da ya halaka.

CP Olokode ya ce ana kokarin gano sauran masu laigin, inda ya bayar da tabbacin cewa za a kai su kotu domin fuskantar doka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel