An kashe mutane 5, an kona gidaje sakamakon arangama tsakanin makiyaya da manoma a Ogun

An kashe mutane 5, an kona gidaje sakamakon arangama tsakanin makiyaya da manoma a Ogun

  • Akalla mutane 5 sun rasu bayan wani rikici ya hada manoma da makiyaya a karamar hukumar Imeko-Afon da ke karkashin jihar Ogun
  • Sakamakon fadan an babbake gidaje, rumbunan masara, babura, shanu da sauran tsadaddun abubuwa a ranar Laraba da Alhamis
  • Shigen hakan ya auku a shekarar da ta gabata ta wuraren Yewa inda rikicin nasu ya yi sanadin rayuka da dama

Jihar Ogun - A kalla mutane 5 ne suka rasa rayyukansu a fada tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Imeko-Afon a Jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

An kuma kona gidaje, rubun abinci, babura da wasu kayayyaki masu muhimmanci yayin rikicin.

An kashe mutane 5, an kona gidaje sakamakon arangama tsakanin makiyaya da manoma a Ogun
Rikici ya barke tsakanin makiyaya da manoma a Ogun, an kashe mutum 5, an yi kone-kone. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Daily Trust ya rahoto yadda rikicin ya fara aukuwa ranar Laraba bayan wasu makiyaya da manoman Ohori suka fara fadan zubar da jini a kauyen Idofa, inda aka yi asarar mutane da dukiyoyin miliyoyin naira.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manoman ne suka fara halaka Fulani da shanunsu

An gano yadda mutane daga garin Aworo a karamar hukumar Yewa ta arewa suka fatattaki wasu makiyaya daga kauyen Idofa zuwa Imeko har suka halaka mutane 3 daga cikinsu da shanunsu.

Mutanen Aworo sun fusatar da Fulanin, daga nan suka far wa gonakinsu da hanyoyin ruwa ta hanyar baza shanunsu don suyi kiwo; abinda gwamnatin jihar ta hana.

Majiyoyi daga kauyakun sun shaida yadda mutane da dama suka tsere don gudun su halaka.

Wata majiya ta bayyana yadda mutanen Aworo suka halaka makiyaya 3 a Idofa; sai dai sun mayar da harin a ranar Alhamis wanda ta janyo mutuwar mutane 2, daya daga cikinsu ma ba a ko gane shi ba saboda babbakar da yasha.

Cikin dare Fulani suka kai wa manoman harin ramuwayar gayya

Kara karanta wannan

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

A cewar majiyar:

“Mutanen Aworo ne suka koro makiyaya daga Yewa ta arewa zuwa Idofa a Imeko. Sun halaka 3 daga cikinsu sannan suka halaka musu shanu.
“A ranar Alhamis kuwa makiyayan suka mayar musu da farmaki da dare. Hakan ya yi sanadin mutuwar mutane 2, sannan sun babbake gidaje da sauran abubuwa. Sai da jami’an ‘yan sanda da Amotekun suka kai dauki.
“Yanzu haka maganar da nake yi mutanen Ohori sun ji raunuka, daruruwansu kuma sun tsere garin Imeko. Muna bukatar taimakon gwamnatin tarayya don tallafa wa ‘yan gudun hijiran.”

Kakakin ‘yan sanda ya ce har yanzu basu kama kowa ba

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar amma ya ce kawo yanzu babu wanda suka kama.

A cewar Oyeyemi:

“Mun samu labari akan mummunan lamarin da ya auku kuma muna bincike a kai. Mun kira duk masu ruwa da tsaki har da na anguwar Fulanin inda suka ce basu san dalilin rikicin ba.

Kara karanta wannan

Kano ce jiha mafi zaman lafiya a Najeriya: Jerin adadin mutanen da aka kashe a 2021

“Muna bincike don kawo garanbawul akan harin kada ya kara maimaita kansa. Kuma yanzu haka jami’an ‘yan sanda suna anguwannin suna bayar da tsaro bisa umarnin kwamishina.”

Ya ce har yanzu ba a kama kowa ba amma suna ci gaba da kokarin ganin an kama duk mai hannu a harin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel