Tambuwal ya yi watsi da rahoton NBS, ya ce jiharsa ba ita ce mafi fatara da talauci a Najeriya ba

Tambuwal ya yi watsi da rahoton NBS, ya ce jiharsa ba ita ce mafi fatara da talauci a Najeriya ba

  • Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto ya caccaki rahoton hukumar kididdiga ta kasa, NBS, kan yadda ta ce jihar ta fi kowacce talauci da fatara a Najeriya
  • Tambuwal ya ce jiharsa ce cibiyar samar da albasa wacce ke noman albasar da ta kai N1 zuwa N2 biliyan a shekara bayan sauran noman da suke yi
  • Aminu Waziri Tambuwal ya ce hatta dabbobin jiharsa sun kai 7 miliyan, wadanda kuwa sun fi jama'ar jihar yawa

Sokoto - Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya yi watsi da rahoton hukumar kidididiga ta kasa inda ta bayyana jihar sokoto a matsayin jihar da ta fi kowacce talauci da fatara duk da kasantuwar ta cibiyar samar da albasa ta kasar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Tambuwal ya yi maganar ne yayin karbar bakuncin shugaban Media Trust Limited (MTL), Malam Kabiru Yusuf, wanda ya kai masa ziyara a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Tambuwal ya yi watsi da rahoton NBS, ya ce jiharsa ba ita mafi fatara da talauci a Najeriya ba
Tambuwal ya yi watsi da rahoton NBS, ya ce jiharsa ba ita mafi fatara da talauci a Najeriya ba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Ban san me yasa suke cewa Sokoto ce jiha mafi talauci ba, da wadanne mizanin suka auna hakan?
"Mun san cewa da yawan mutanen mu manoma ne, a takaice Sokoto ce jihar da ta fi kowacce noman albasa a kasar nan. Muna samar da albasa ta N1 zuwa N2 biliyan a kowacce shekara. Na san mutum daya da ke noman albasar da ta kai ta naira miliyan dari 7.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ta yaya za ku kira jihar da kusan dukkan jama'ar ta ke noma a dukkan shekarar a matsayin matalauta. Dole ne akwai dalilin hakan. Muna da dabbobin kiwo sama da miliyan 7, sun fi mutane yawa a jihar, amma har yanzu matalauta ake kallon mu," yace.

Gwamnan ya jinjina wa hukumar MTL kan yadda ta kafa gidan talabijin na Trust, wanda yace zai taimaka wurin sanar da duniya gaskiyar abinda arewa ta ke ciki da kasar baki daya kamar yadda jaridar ke bayyanawa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Wani jirgin saman Arik daga Legas ya yi hadari, ya sauka a Asaba

"Ina kallon shirye-shiryen ku kuma ina yabawa da nagartar labarun ku," yace.

Tun farko, Yusuf ya ce ya je jihar ne domin zantawa da gwamnan kan sabon gidan talabijin na Trust wanda ke watsa labarai kuma sun bukaci cigaban goyon bayansa da gwamnatinsa.

Jihohi 10 da suka fi talauci a Najeriya

A wani labari na daban, hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta yi amfani da wasu abubuwa a matsayin mizanin auna yawan talauci a jihohin Najeriya, inda ta fitar da jerin jihohi da kuma matakin da suke kai a yawan talauci.

Yawancin jihohin Najeriya na fama da talauci ne saboda rashin shugabanci nagari, almundahana da almuubazzaranci da dukiyar gwamnati da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel