IBB: Mu waliyyai ne akan 'yan siyasar yanzu idan ana maganar rashawa

IBB: Mu waliyyai ne akan 'yan siyasar yanzu idan ana maganar rashawa

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce su waliyyai ne a lokacin da suke kan mulki
  • IBB ya fadi hakan ne a lokacin da yake martani kan yawan rashawa a zamaninsu da kuma yanzu
  • Ya ce ya sauke gwamna saboda badakalar N300,000 a mulkinsa amma sai ga shi a yanzu ana satar biliyoyin naira

Minna, Niger - Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce idan aka kwatanta yawan cin hanci da rashawa da ke yi a Najeriya yanzu, toh su waliyyai ne a lokacin da yake mulki.

Babangida ya bayyana hakan ne a wata hira da Trust TV a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, wanda manema labarai suka sanya ido.

Ya ce a lokacin da yake kan mulki, ya tsige gwamna saboda badakalar N300,000 amma sai ga shi a yanzu yan siyasa na yin sama da fadi kan biliyoyin naira hankali kwance.

Kara karanta wannan

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

IBB: Mu waliyyai ne akan 'yan siyasar yanzu idan ana maganar rashawa
IBB: Mu waliyyai ne akan 'yan siyasar yanzu idan ana maganar rashawa Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na sallami gwamna saboda badakalar N300,000. A yanzu akwai mutane da muke karantawa a jaridu, mun gode Allah akwai jaridun karantawa sannan akwai shafukan soshiyal midiya da sauransu; wadanda suke satar naira biliyan 2, naira biliyan 3.
"Kuma babu wanda ke cewa su masu rashawa ne; sai mu kawai saboda mu sojoji ne, shikenan.
“Ina jadadda cewa mu salihai ne idan ka kwatanta mutumin da ake zargin a da da satar naira biliyan 3 da wanda ke da N300,000; ina ganin mu salihai ne."

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

Da farko mun ji cewa IBB ya sake bayar da wasu muhimman shawarwari kan yadda gwamnati za ta yi nasara a yaki da cin hanci da rashawa.

IBB ya ce:

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

"Na bayar da wani shawara amma saboda ya fito daga gareni, babu wanda ke son shi, babu wanda ke son jin shi: A gano wuraren cin hanci da rashawa sannan a magance su daga tushe. Na karanta daya daga cikin jaridu inda alkali ke korafin cewa ba a biyansu albashi mai kyau kuma hakan tabbataccen tushe ne na cin hanci da rashawa.
"A duk inda kake da tsari da ke da masu jan ragama da yawa dole za a samu cin hanci da rashawa. Don haka, abun da muke kokarin yi, muna shawartan gwamnati da kada ta shiga cikin abubuwa kamar sarrafa kayayyaki; duk wani abu da ya shafi sai na zo wajenka kuma za ka rika tunanin kana yi mani alfarma ne, don haka wata kila in rama shi, haka abin yake."

Asali: Legit.ng

Online view pixel