Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sako daliban jami'ar Nasarawa da suka sace

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sako daliban jami'ar Nasarawa da suka sace

  • Dalibai hudu na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Lafia, jihar Nasarawa da aka sace a ranar Alhamis, 13 ga Janairu, sun shaki iskar 'yanci
  • Shugaban jami'ar, Farfesa Shehu Abdul Rahman, ya tabbatar da sako daliban a sa'o'in karshe na ranar Asabar da ta gabata
  • Ya ce an duba lafiyar daliban kuma ya mika sakon godiyarsa ga hukumomin tsaro kan taimakon gaggawa da suka bayar har yayi sanadin samo daliban

Lafia, Nasarawa - Dalibai hudu na jami'ar tarayya da ke Lafia a jihar Nasarawa da aka sace a ranar Alhamis, sun shaki iskar 'yanci.

Hudu daga cikin daliban jami'ar, wadanda aka sace a wajen farfajiyar jami'ar, an sak su a sa'o'in karshe na ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba a da daliban jami'ar Tarayya a Nasarawa

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sako daliban jami'ar Nasarawa da suka sace
Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sako daliban jami'ar Nasarawa da suka sace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban jami'ar, Farfesa Shehu Abdul Rahman, wanda ya yi magana ta bakin jami'in hulda da jama'ar jami'ar, Abubakar Ibrahim, ya tabbatar da sako wadanda aka sacen a ranar Lahadi.

A yayin yaba wa gwamnatin jihar Nasarawa da jama'a kan gudumawarsu, addu'a da goyon baya ga jami'ar yayin da suke cikin halin kakanikayi, ya gode wa jaridar Daily Trust kan yadda ta ke yada labaran jami'ar.

“Hukumar jami'ar tarayya da ke Lafia, ta na farin cikin sanar da cewa an sako dalibai hudu na jami'ar da aka sace a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu."
"Shugaban jami'ar na mika sakon godiyarsa na musamman ga hukumomin tsaro kan yadda suka bayar da taimakon gaggawa wanda hakan ne ya taimaka wurin dawowar daliban," yace.

Shugaban jami'ar ya ce bayan sako su, an duba lafiyar daliban kuma an gano suna cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

Ya kara da yin kira ga daliban da su kasance cikin kwanciyar hankali kuma su cigaba da al'amuransu kamar yadda suka saba.

Shugaban jami'ar ya kara da tabbatar wa da iyaye, dalibai da jama'a cewa suna bai wa rayuka da kadarori kariya a jami'ar yadda ya dace.

Bayan kwashe wata 7 a hannun ƴan ta'adda, ɗaliɓan FGC Kebbi sun shaƙi iskar ƴanci

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kebbi ta ce an sako dalibai 30 da malami daya na kwalejin gwamnatin tarayya (FGC) Birnin Yawuri wadanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.

Yahaya Sarki, hadimin gwamna Atiku Bagudu ne ya tabbatar da nasarar a ranar Asabar, TheCable ta ruwaito.

A watan Yunin 2021, wasu ‘yan bindiga sun afka makarantar inda su ka yi garkuwa da dalibai da dama da malamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel