Bayan kwashe wata 7 a hannun ƴan ta'adda, ɗaliɓan FGC Kebbi sun shaƙi iskar ƴanci

Bayan kwashe wata 7 a hannun ƴan ta'adda, ɗaliɓan FGC Kebbi sun shaƙi iskar ƴanci

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da sakin dalibai 30 da malami daya na kwalejin gwamnatin tarayya (FGC) Birnin Yauri bayan an yi garkuwa da su
  • Yahaya Sarki, hadimin gwamna Atiku Bagudu na musamman na bangaren labarai ya tabbatar da wannan nasarar a ranar Asabar
  • Dama tun watan Yunin 2021 wasu ‘yan bindiga a kan baburansu su ka afka makarantar inda su ka yi garkuwa da dalibai da dama da malamai

Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta ce an sako dalibai 30 da malami daya na kwalejin gwamnatin tarayya (FGC) Birnin Yawuri wadanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.

Yahaya Sarki, hadimin gwamna Atiku Bagudu ne ya tabbatar da nasarar a ranar Asabar, TheCable ta ruwaito.

Bayan kwashe wata 7 a hannun ƴan ta'adda, ɗaliɓan FGC Kebbi sun shaƙi iskar ƴanci
Bayan kwashe wata 7 a hannun ƴan ta'adda, ɗaliɓan FGC Kebbi sun shaƙi iskar ƴanci. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A watan Yunin 2021, wasu ‘yan bindiga sun afka makarantar inda su ka yi garkuwa da dalibai da dama da malamai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan watanni 6, an sako daliban kwalejin da aka sace a Kebbi

‘Yan bindigan sun afka makarantar a baburansu inda su ka yi musayar wuta da ‘yan sanda, dalilin haka suka ji wa dalibai raunuka sannan wani ya mutu take yanke.

Sarki ya ce an kai wadanda su ka samu raunukan asibiti daga bisani kuma aka sada su ga iyayensu.

“Yau ranar Asabar, 68 ga watan Janairun 2022, an sako dalibai 30 na FGC Birnin Yawuri na jihar Kebbi,” a cewar Sarki.
“Za a duba lafiyarsu daga bisani sai a sada su da iyayensu.
“Muna godiya ga jami’an tsaron da su ka taimaka har aka kwato su sannan ina taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar wannan nasarar," yace.

A watan Oktoba, TheCable ta ruwaito yadda aka sako dalibai 30 da malamai 3 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

'Dan Sanda Abokin Kowa: Lokuta 4 da ƴan sandan Najeriya suka yi wa mutanen da basu sani ba manyan abin alheri

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

A wani labari na daban, an sako malaman makaranta da daliban kwalejin aikin gona da kimiyyar dabbobi ta jihar Zamfara dake Bakura.

Wata majiya daga tushe na kusa da gwamnatin jihar Zamfara da ta nemi a sakaya sunanta ta sanar wa jaridar Punch cewa za a kawo su gidan gwamnati gobe Juma'a 27 ga watan Agusta, amma, ya ki yin karin bayani.

Idan za a iya tunawa a ranar 16 ga watan Agusta, 2021 wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari kwalejin tare da sace mutane 19 da suka hada da ma'aikata uku, dalibai 15 da direba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel