Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari

Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani a kan rikicin kabilanci da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a jihar Filato
  • Buhari ya gargadi kungiyoyin da abun ya shafa da su guji daukar doka a hannunsu da sunan ramuwar gayya
  • Shugaban kasar ya yaba ma Gwamna Simon Lalong kan yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da lamarin zuwa yanzu

Filato - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi bangarorin da ke fada da junansu a rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato da su guji daukar doka a hannunsu da sunan ramuwar gayya.

Buhari ya nuna bakin cikinsa kan sabbin kashe-kashen da ya wakana a karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato, inda yace lamarin ya saba yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin kabilar Irigwe da Fulani a yankin.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari
Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shugaban kasara cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu a Abuja, ya ce a matsayin al'umma, babu kafa na yin irin wannan tashin hankali da ake gani a jihar.

Da yake bayyana rikicin a matsayin abun da ba zai karbu ba, shugaban kasar ya ce lamarin bai yi daidai da manufar yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin kabilun yankin biyu ba, rahoton Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

"Zuciyana na tare da iyalan wadanda abun ya shafa a wannan lokaci na bakin ciki. Allah ya ji kansu."

Ya bukaci garuruwa daban-daban da ke yankin, musamman kungiyar addinai daban-daban na jihar Filato da su yi duk mai yiwuwa domin wanzar da yarjejeniyar zaman lafiya da kuma hana shi tarwatsewa.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shehu Sani ya bayyana matsayinsa a kan tsarin mulkin karba-karba

"Kowace kungiya da ke daukar doka a hannunsu suna ikirarin ramuwar gayya be. A matsayin al'umma, babu kafa na yin irin wannan tashin hankali. Wannan ba abin yarda ba ne.”

Shugaban kasar ya yaba ma Gwamna Simon Lalong kan yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da lamarin zuwa yanzu, rahoton Channels TV.

Bayan rikici ya lafa a Filato, an sake hallaka Bayin Allah a wani danyen harin tsakar dare

A gefe guda, mun kawo a baya cewa kungiyar Irigwe Development Association ta koka kan kisan mutanenta da ta ce an yi a kauyen Ancha, yankin Miango a karamar hukumar Bassa.

Rahoton da muka samu a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2021 shi ne an kashe mutum 18 a Ancha a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kasar Rigwe.

Mai magana da yawun bakin kungiyar Irigwe Development Association, Mr. Davidson Malison ya aikawa jaridar Vanguard jawabin da suka fitar bayan harin.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel