Tsohon Atoni Janar na jihar Kaduna, Rabo Barde, ya mutu

Tsohon Atoni Janar na jihar Kaduna, Rabo Barde, ya mutu

  • Tsohon Atoni Janar na jihar Kaduna, Barista Rabo Barde, ya kwanta dama
  • Rahotanni sun ce marigayin ya mutu ne a ranar Litinin 3 ga watan Janairu sannan za a binne shi a ranar 15 ga watan Janairu
  • An kuma tattaro cewa Barde ya mutu ne a cikin baccinsa yayin da yake farfadowa daga wata rashin lafiya

Kaduna - Tsohon Atoni Janar na jihar Kaduna, Barista Rabo Barde, ya mutu yana da shekaru 72 a duniya.

Barde ya mutu ne a ranar Litinin, 3 ga watan Janairu yayin da yake farfadowa daga rashin lafiya, rahoton Punch.

Tsohon Atoni Janar na jihar Kaduna, Rabo Barde, ya mutu
Tsohon Atoni Janar na jihar Kaduna, Rabo Barde, ya mutu Hoto: The Punch
Asali: UGC

Za a binne marigayin a mahaifarsa ta Kafanchan a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu.

A cewar wata sanarwa da Manjo Livinus Sambo mai ritaya ya fitar a madadin iyalan marigayi, Barde ya mutu ne a cikin baccinsa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shahararren tsohon shugaban PDP ya rasu a wata jihar arewa

Sambo ya ce:

"Marigayin ya mutu hankali kwance a cikin baccinsa yayin da yake farfadowa daga rashin lafiya a ranar 3 ga watan Janairun 2022.

"Za a yi bikin mutuwarsa ne a cocin St. Pius Catholic Church, Lusawa Ungwan Romi a ranar Juma’a, 14 ga watan Janairu, 2022, yayin da za a dauki gawarsa daga Asibitin St. Gerald a ranar Asabar 15 ga Janairu, 2022 zuwa mahaifarsa a garin Ungwan Fari Kaninkon Kafanchan, karamar hukumar Jemaa."

Barde wanda ya kasance tsohon kwamishinan shari'a a jihar Kaduna ya mutu ya bar yara biyar da jikoki hudu, rahoton Vanguard.

Ya kuma kasance tsohon lauyan jam'iyyar Peoples Democratic Party ( PDP).

Shahararren tsohon shugaban PDP ya rasu a wata jihar arewa

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa tsohon Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Taraba, Abdulmumuni Vaki, ya rasu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Iyalin mamaci sun mayarwa Gwamnati kudin Albashin shekara 11 da ya karba ba ya zuwa aiki

Vaki ya rasu yana da shekaru 54 bayan ya yi fama da jinya a cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Jalingo, babbar birnin jihar Taraba. Ya rasu ne a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu.

Marigayin ya yi shugabancin jam’iyyar PDP a jihar sau uku kuma ya kasance mamba a hukumomin tarayya da na jihar Taraba da dama.

A kwanan nan ne Gwamna Darius Ishaku ya nada shi a matsayin mamba a hukumar aikin hajji ta jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel