Da dumi-dumi: Shahararren tsohon shugaban PDP ya rasu a wata jihar arewa

Da dumi-dumi: Shahararren tsohon shugaban PDP ya rasu a wata jihar arewa

  • Allah ya yiwa tsohon Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Taraba, Abdulmumuni Vaki, rasuwa
  • Vaki ya rasu ne a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, bayan ya yi fama da doguwar jinya
  • Za a yi jana'izarsa a mahaifarsa ta Gembu, hedkwatar karamar hukumar Sardauna a yau Alhamis, 13 ga watan Janairu

Taraba - Tsohon Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Taraba, Abdulmumuni Vaki, ya rasu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Vaki ya rasu yana da shekaru 54 bayan ya yi fama da jinya a cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Jalingo, babbar birnin jihar Taraba. Ya rasu ne a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu.

Da dumi-dumi: Shahararren tsohon shugaban PDP ya mutu a wata jihar arewa
Da dumi-dumi: Shahararren tsohon shugaban PDP ya mutu a wata jihar arewa Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Marigayin ya yi shugabancin jam’iyyar PDP a jihar sau uku kuma ya kasance mamba a hukumomin tarayya da na jihar Taraba da dama.

Kara karanta wannan

2023: Babban jami'in INEC ya ajiye aikinsa, ya shiga APC don yin takarar gwamna a jihar Arewa

A kwanan nan ne Gwamna Darius Ishaku ya nada shi a matsayin mamba a hukumar aikin hajji ta jihar Taraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marigayi Vaki ya rasu ya bar matan aure uku da yara hudu.

TVC News ta rahoto cewa tuni magoya bayan mamacin suka yi turuwan zuwa gidansa da ke Jalingo domin taya iyalan alhini.

Za a binne shi a mahaifarsa ta Gembu, hedkwatar karamar hukumar Sardauna a yau Alhamis, 13 ga watan Janairu.

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na wani tsohon shugabanta

A wani labari makamancin haka, mun kawo a baya cewa tsohon Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo, Hafeez Tijani Adiaro, ya rasu.

Sahara Reporters ya rahoto cewa Adiaro ya rasu ne a yammacin ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo

An tattaro cewa marigayin ya bayar da cikakken lokacinsa ga siyasa a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Oyo, Rasheed Ladoja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel