Gwamna Yahaya Bello ya fatattaki masu karbar haraji daga titunan Kogi

Gwamna Yahaya Bello ya fatattaki masu karbar haraji daga titunan Kogi

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fatattaki masu tsare manyan titunan jihar suna karbar haraji ba bisa ka'ida ba
  • An gano cewa, masu karbar harajin sun tsare tawagar gwamnan cikin wani dogon layi, wanda hakan ya matukar kunyata gwamnan
  • A take ya fito tare da bayar da umarnin a cire dukkan wasu shinge da ake sakawa a kan titunan kuma ya haramta wa gama-gari karbar harajin

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a ranar Alhamis ya dakile dukkan al'amuran karbar haraji ba bisa ka'ida ba kuma ya bayar da umarnin cewa dukkan shingen kan tituna da aka saka a babban titin Okene zuwa Lokoja a cire shi.

Hakazalika, gwamnan ya bayar da umarnin cire dukkan wuraren da aka tsare tare da rufewa na kan titunan jihar saboda karbar harajin da ba bisa ka'ida ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

Gwamna Yahaya Bello ya fatattaki masu karbar haraji daga titunan Kogi
Gwamna Yahaya Bello ya fatattaki masu karbar haraji daga titunan Kogi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Gwamna Bello ya sanar da cewa, al'amuran su suna da matukar bayar da takaici ga masu ababen hawa da kuma masu amfani da titunan jihar.

An gano cewa, Gwamnan Yahaya Bello ya makale a wani dogon layin ababen hawa a kan babban titin Okene zuwa Lokoja a safiyar Alhamis, duk a karkashin sakacin masu karbar harajin, lamarin da ya matukar kunyata shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya sauka daga motar sa kuma ya umarci wani jami'in tsaro mai kula da lafiyar sa da ya tabbatar da an cire shingen kan titin a take, bayan tattaunawa da yayi da masu karbar harajin ba bisa ka'ida ba.

"Al'amuran masu karbar harajin a kan tituna ya zama abinda ya zama domin ya na matukar takura wa direbobin tasi da sauran ababen hawa saboda yadda su ke kallafa haraji ga jama'a," Bello yace.

Kara karanta wannan

Har yanzu haramun ne safarar fatar jaki zuwa kasashen waje, Gwamnatin Najeriya

Gwamnan ya ja kunnen cewa, ba zai lamunci irin wannan shirmen ba a jihar, inda ya jaddada cewa masu karbar haraji na ka'ida daga hukumomin da ya dace ne kadai aka amince su karba harajin.

Wani matafiyi mai suna Joseph Makinde, wanda ya hadu da masu karbar harajin a kan babbar hanyar, ya ce sun kwashe sa'o'i suna buga dogon layin da aka kirkira kafin isowar gwamnan wanda ya bukaci a bar su su wuce.

Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya saki matarsa ta uku, Hafiza

A wani labari na daban, Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya saki matarsa ta uku mai suna Hafiza a cewar wasu rahoto da LIB ta wallafa.

Vanguard ta ruwaito cewa an tabbatar da hakan kwanaki kadan da suka wuce a jawabin da ya yi yayin da ya ke karbar lambar yabo daga Cibiyar Kungiyoyin Mata na Kasa (NCWS).

Gwamnan ya mika godiya ga matansa, Hajiya Amina Yahaya Bello da kuma First Lady Hajiya Rashida Bello a jawabinsa na wurin taron amma bai ambaci Hajiya Hafiza ba. Kawo yanzu ba a tabbatar da dalilin da yasa gwamnan ya sake ta ba.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

Wasu daga cikin magoya bayan gwamnan sun bayyana ra'ayoyinsu kan labarin da ya bazu na cewa ya saki matarsa ta uku, Hafiza.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel