Har yanzu haramun ne safarar fatar jaki zuwa kasashen waje, Gwamnatin Najeriya

Har yanzu haramun ne safarar fatar jaki zuwa kasashen waje, Gwamnatin Najeriya

  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta jaddada cewa har yanzu haramun ne safarar fatar jaki zuwa kasashen ketare inda ake amfani da su wurin magunguna da wasu abubuwan
  • Shugaban hukumar NAQS, Dr Vincent Isegbe, ne ya fitar da sanarwar a matsayin martani kan rahoton da aka fitar kan kuskure na cewa an dage haramcin
  • Gwamnatin tarayyar ta saka haramci ne kan safarar fatar jakan saboda adadin jakunan da ake da su a Najeriya sun tasan ma karewa

Abuja - Hukumar killace kayyakin noma da kiwo ta Najeriya, NAQS, ta jadada cewa har yanzu fatar jakuna suna cikin jerin abubuwan da aka haramta safarar su zuwa kasashen waje, Daily Trust ta ruwaito.

Ta jadada cewa dage haramcin da aka saka wa fatar jakin ya danganta ne kan yawan jakuna da ake da su a kasar wanda har a yanzu suna cikin dabobin da ke fuskantar barazanar karewa a doron kasa.

Kara karanta wannan

FG ta bayyana sharudda 5 da ta gindaya wa Twitter kafin dage dokar haramci

Har yanzu haramun ne safarar fatar jaki zuwa kasashen waje, Gwamnatin Najeriya
FG: Har yanzu haramun ne safarar fatar jaki zuwa kasashen waje
Asali: Facebook

Da ta ke martani kan rahoton 'da aka fitar cikin kuskure da ke cewa NAQS ta dage haramci kan safarar fatar jaki', shugaban hukumar na kasa, Dr Vincent Isegbe, cikin sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban watsa labarai na hukumar da aka fitar a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce hukumar ta gana da masu ruwa da tsaki a Satumba don tsara hanyar da za a kara adadin jakuna da hanyar kiwonsu don kada su kare a doron kasa.

Har sai adadin jakuna sun karu a Najeriya za a janye haramcin, FG

Dr Isegbe ya kara da cewa gwamnati za ta cire fatar jakuna daga jerin abubuwan da ta haramta safarar su ne kadai idan an samu karuwar jakuna sosai a Najeriya, rahoton Daily Trust.

An samu raguwar jakuna a Najeriya ne saboda bukatar su da aka yi a kasashen nahiyar Asia.

Kara karanta wannan

Jami’ar Kano Ta Ɗage Yin Jarrabawa Saboda Yajin Aikin Masu Baburan A-Daidaita-Sahu

Ana amfani da fatar jakunan ne wurin hada magunguna da ake ikirarin suna magance cututuka da dama.

Cire tallafin man fetur: Ku kasance cikin shirin yin zanga-zanga, NLC ga mambobinta

A wani labarin, Kungiyar kwadagon Najeriya, ta umarci mambobinta, kungiyoyin da ke karkashinta da sauran ma’aikatan gwamnati su shirya yin zanga-zangar da za a yi a fadin kasa daga ranar 27 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Fabrairu kan shirin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.

Kungiyar ta bukaci duk kungiyoyin da ke karkashinta a fadin kasar nan da su umarci mambobinsu don tabbatar da zanga-zangar da za a yi ta kasa baki daya, The Punch ta ruwaito.

Wannan shi ne babban dalilin yin taron wanda shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya yi da shugabannin kungiyoyin da ke karkashin Kungiyar kwadagon a gida da ke Abuja ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel