Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya saki matarsa ta uku, Hafiza
- Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya saki matarsa ta uku Hajiya Hafiza
- An tabbatar da hakan ne bayan gwamnan ya yi jawabi a wurin taro ya ambaci matansa amma banda Hafiza
- Magoya bayan gwamnan a kafafen sada zumunta suna ta kira ga yan mata su fara takarar cike gurbin
Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya saki matarsa ta uku mai suna Hafiza a cewar wasu rahoto da LIB ta wallafa.
Vanguard ta ruwaito cewa an tabbatar da hakan kwanaki kadan da suka wuce a jawabin da ya yi yayin da ya ke karbar lambar yabo daga Cibiyar Kungiyoyin Mata na Kasa (NCWS).
DUBA WANNAN: FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa
Gwamnan ya mika godiya ga matansa, Hajiya Amina Yahaya Bello da kuma First Lady Hajiya Rashida Bello a jawabinsa na wurin taron amma bai ambaci Hajiya Hafiza ba.
Kawo yanzu ba a tabbatar da dalilin da yasa gwamnan ya sake ta ba.
Wasu daga cikin magoya bayan gwamnan sun bayyana ra'ayoyinsu kan labarin da ya bazu na cewa ya saki matarsa ta uku, Hafiza.
KU KARANTA: 'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria
Magoya bayan a dandalin sada zumunta sun rika kira ga 'yan mata su fara takara domin samun shiga wurin gwamnan na Jihar Kogi a matsayin mata na uku da hudu.
Sai dai kawo yanzu babu wani jawabi a hukumance da ke gasgata ko karyata batun rabuwar gwamnan da matarsa ta uku.
A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng